’Yancin da Gwamnatin Tarayya ta ba kananan hukumomi ya yi daidai’

Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi (ALGON) reshen Jihar Kaduna, kuma Shugaban Karamar Hukumar Soba, Alhaji Muhammad Mahmoud Aliyu Gimba ya ce ’yancin cin gashi kai da Gwamnatin Tarayya ta ba kananan hukumomi abu ne da ya dace saboda kananan hukumomin ne suka fi kusa da jama’a. Shugaban ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da […]

’Yancin da Gwamnatin Tarayya ta ba kananan hukumomi ya yi daidai’
’Yancin da Gwamnatin Tarayya ta ba kananan hukumomi ya yi daidai’

Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi (ALGON) reshen Jihar Kaduna, kuma Shugaban Karamar Hukumar Soba, Alhaji Muhammad Mahmoud Aliyu Gimba ya ce ’yancin cin gashi kai da Gwamnatin Tarayya ta ba kananan hukumomi abu ne da ya dace saboda kananan hukumomin ne suka fi kusa da jama’a.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Maigana.

Alhaji Mahmoud Aliyu, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar ALGON ta Kasa ya ce, kananan hukumomin Jihar Kaduna tuni suka samu ’yancin cin gashin kansu.

Ya ce, lokaci ya yi da kananan hukumomi za su ba marada kunya ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa da za su amfani al’umma. Ya ce duk da an ba su  ’yancin, ba a kyale su kara-zube ba, dole ne sai  gwamnatocin jihohi za su rika sanya ido kan yadda kananan hukumomin ke kashe kudadensu.