’Yancin dan Adam, wanne kuma don me? (2)

Malama A’isha Usman Liman [email protected]  ta ci gaba da muhimmiyar fadakarwa ga al’umma:Duk wadannan fafutuka na neman shugabanci da mulki, dan Adam yana yi ne don tabbatar da wanzuwar ’yancinsa da Allah Ya ba shi a doron kasa; domin yana ganin in ba tare da mulki ba, to ba ’yanci cikakke a gare shi; domin […]

’Yancin dan Adam, wanne kuma don me? (2)

Malama A’isha Usman Liman [email protected]  ta ci gaba da muhimmiyar fadakarwa ga al’umma:
Duk wadannan fafutuka na neman shugabanci da mulki, dan Adam yana yi ne don tabbatar da wanzuwar ’yancinsa da Allah Ya ba shi a doron kasa; domin yana ganin in ba tare da mulki ba, to ba ’yanci cikakke a gare shi; domin zai yi ta haduwa da kalubale masu yawa, kila ma su takura masa har su hana shi samun “damar” da yake da ita ta sarrafa wannan ’Yancin nasa da baiwar da yake da ita, na tafiyar da rayuwarsa a doron duniya.
Haka dai duniya na yaduwa ba dare ba rana kuma kalubalen tabbatar da ’yanci ta hanyar neman shugabanci da mulki yana yaduwa. Wannan shi ne har ya yi musabbabin jefa duniya cikin rudanin tashe-tashen hankula da fadace-fadace nan da can, wanda har ya yi musabbabin kai ta ga yakin duniya na daya da na Biyu.
Tun daga 1941 zuwa 1945, bayan gama yakin duniya na biyu sai shugabannin Amurka, Franklin Roosebelt da Firaministan Ingila Winston Churchill da na Tarayyar Sobiyat (Rasha a yanzu), dake ake kira da “Big Three” (Manya Uku) suka fara taruka, inda suke tattauna hanyoyin samun zaman lafiya a duniya.
Daga wannan tattaunawar da kuma kaifin hankali da zurfin tunani da fatan alheri da suke da shi, sai suka yanke shawarar kirkiro wata majalisa da za ta hada kan kasashen duniya ta dinke wuri daya, domin gudun sake saka duniya cikin yaki karo na uku. An kafa wannan majalisa a watan Afirilu, 1945.
Manufar wannan majalisa kuwa ita ce dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan fadin duniya, samar da zauren tattaunawa ga kasashen duniya don duba manufofinsu da dawo da jituwa da zaman lafiya, ba tare da tashe-tashen hankula ba a fadin duniya, hanyoyin zaman lafiya da samar da gudunmawa ga kasashen da suke da matsaloli, kamar matsalar talauci, cututtuka, muhalli da dai sauransu. A takaice dai wannan majalisar ita ce taswirar duniya da kuma dokokinta kuma yana cikin aikinta, daidaita martabar tattalin arzikin kasashen da ke tasowa, domin rashin tattalin arzikin kasa shi ke janyo rigingimu da ke haddasa yake-yake.
Majalisar dinkin Duniya tana tallafa wa kungiyoyi da gidauniyoyi na cikinta, kai har ma da na wajenta, wadanda suke taimaka wa mutanen kasashensu. Amma babbar manufar majalisar shi ne samar da ’yancin dan Adam ba tare da bambancin fata, yare, da jinsi ko addini ba. Don haka ne ma ta kirkiro ‘Ranar Martabar ’Yancin dan Adam A Duniya’ wadda ake rayawa kowane goma ga Disamba na kowace shekara a duniya. An farashi ne tun daga 1948 kuma majalisar tana da ofishi na Kwamishinan musamman mai kula da ’yancin dan Adam. An kirkiro ofishin ne a 1993. Aikinsa shi ne na kula da dukkan dokokin wanzar da ’yancin dan Adam kuma da dukkan fitinun da za su iya tasiri su hana dan Adam ’yancinsa da Allah Ya ba shi, kai har ma da wanda ya kirkiro wa kansa, domin bayan ’yancin da Allah Ya ba shi, ya kara wa kansa nasa ’yancin kamar haka:
Kowane dan Adam yana da ’yancin magana da bayyana damuwarsa, ’yancin yin addininsa, ’yancin abin da yake so da kuma ’yancin aminta shi daga jin tsoro.
Wadannan ’yanci, duk lokaci daya aka kirkire su da Majalisar dinkin Duniya, duk dai domin samar da martabar zaman lafiya a duniya, domin dan Adam ya sami ’yancin walwala a duniya.
Lallai duniya ta samu babban ci gaba a sanadiyyar kirkiro wannan majalisa, ta fuskar zaman lafiya da kwanciyar hankali, samar da ’yanci ga dan Adam, gyaruwar tattalin arzikin mafiya yawan kasashen duniya, kula da lafiyar mutane, kula da ilimi, kula da halin da muhallin kasashenta ke ciki, samar da babbar kotu domin hukunci ga kasashe masu manyan laifuka, tabbatar da tsaro ga kasashenta, samar da tallafi ga kasashen da suke a cikin matsaloli ko wadanne iri, samar da ’yanci ga kasashen da suke cikin kangin mulkin mallaka, da dai sauran ci gaba manya da kanana, ga kuma uwa uba, yada manhajar dimokuradiyya a cikin siyasar duniya, domin kuwa ba karamin ’yanci ta samar wa dan Adam ba ta fuskar siyasa kuma ba karamin zaman lafiya ta wanzar ba a tsakanin kasashen da suka kaddamar da ita ba. Ita ce ta ke ba dan Adam ’yancin zabar wa kansa shugaban da yake ganin shi ne ya cancanta ya shugabance shi.
Wadannan da ma wasu da ba mu ambata ba, su ne ci gaba da wanzuwar Majalisar dinkin Duniya ya samar a wannan duniya, wanda a sanadiyyar haka ya sa duniya samun gawurtaccen arziki mai yawa a kowane sako da lungu na duniya. Misali, samun ci gaban ilmin kimiyya da fasaha, wadanda ke bunkasa cikin sauri ba dare ba rana. Wannan ilimin ba karamin tasiri yake da shi ba, domin a sanadiyyarsa ya sa dan Adam samun saukin rayuwa ta hanyar sadarwa, sufuri, lafiya, muhalli, abinci, ilimi, kai da duk dai zamantakewar dan Adam. Duniya ta yi dadi, ta yi kyau kwarai, an samu karuwar wayewar kai, da dai sauransu.
Don haka, ba karamar godiya za mu yi wa wadannan manyan sugabannin duniya ba, da wannan zurfin tunanin nasu na kirkiro wannan babbar majalisa mai albarka
 Me ke faruwa a yanzu? Kamar misalin shekaru saba’in da wani abu da suka wuce da kafuwar wannan majalisa, ba ta ma kai shekaru 100 da kafuwa ba amma sai ga shi duniya tana neman ta koma a kan turbar da ta baro a can baya, na tashe-tashen hankula da rikice-rikicen siyasa da na kabilanci da na addini da na rabon iyakar kasashe da suke haddasa fadace-fadace da fittintunu a duniya. Wadannan fitintunu sai kara ruruwa suke yi a kullum, kusan kullum idan za ka saurari wata kafar sadarwa, ko ta yada labarai sai ka ji sabon tashin hankali ya bayyana a wani wuri. Kuma abin haushi, wadannan tashe-tashen hankula kusan duk sun fantsama a dukkan kasashen Duniya. Kuma ma karin abin haushin, yanzu sai gasar kere-keren makamai manya da kanana ke ta karuwa, ga kuma takama ga wadanda suke ganin sun mallaki manyan makamai. Sai tsokane-tsokane suke, don su sami sararin gwada  makaman.
Shin wai idan akwai cikakken zaman lafiya a duniya, me ya kawo gasar tara makamai, har da masu guba? Wadanda idan suka tashi, suna iya illata Duniya ga baki dayanta? Amsar ke nan, saboda a wannan zamanin shi ne kokawar fin karfi da ake yi a da can. Yanzu duk kasar da ta fi yawan makamai masu karfi da guba, za a yi ta jin tsoronta, ana jin shakkarta, ana kuma girmama ta na dole, koda ba a so ba. Daga nan kuma ta sami hanyar da za ta yi ta yi wa sauran kasashen da ba su mallaka ba fin karfi da mazurai da danniyar ’yancin da suke da shi, sai kuma kasar mai manyan makamai da zarar ta lura da wannan yanayin na jin tsoronta da ake yi, ba za ta sake barin a zauna lafiya ba. Ta rika kirkiro gutsiri-tsoma ke nan, tana tilasta wa kananan kasashe har sai ta kure hakurinsu, sun fara nuna rashin yardarsu da tsare-tsarenta a kansu. To daga wannan lokacin shi ke nan gwamnatin wannan kasar ta jawo wa kanta, don daga ranar za a fara neman su waye masu adawa da ita? Sai a fara tunzura su, ana biyan su kudi suna fito-na-fito da hukuma. Abu wasa-wasa har karamar magana ta zama babba. Shi ke nan an haddasa mata makiya ’yan zanga-zanga, ana taimaka musu da kudi da makamai har sai an ture gwamnatin wannan kasar, an kafa ta ’yan tawaye. Ita kuwa babbar kasar mai agazawa da makamai sai a ce ta yi nasara, domin duk ragamar gudanarwar kasar zai kasance a hannunta, sai abin da ta tsara ta wanzar – arziki da tsaro da shugabancin kasar sai yadda ta tsara ta gabatar. Shi ke nan wasa-wasa an sake jefa wannan kasa cikin mulkin mallaka, sai yadda aka yi da ita.