’Yancin dan Adam, wanne kuma don me? (3)

A yau Malama A’isha Usman Liman [email protected]  ta ci karkare muhimmiyar fadakarwa ga al’umma da cewa:An manta da ’yancin da aka ba kasar a can baya da ’yancin mutanen kasar da suke da shi na zaben shuwagabanin da suke ganin su suka cancanta su ja ragamar mulkinsu. An manta da ’yancin da suke da shi […]

’Yancin dan Adam, wanne kuma don me? (3)

A yau Malama A’isha Usman Liman [email protected]  ta ci karkare muhimmiyar fadakarwa ga al’umma da cewa:
An manta da ’yancin da aka ba kasar a can baya da ’yancin mutanen kasar da suke da shi na zaben shuwagabanin da suke ganin su suka cancanta su ja ragamar mulkinsu. An manta da ’yancin da suke da shi na su zauna lafiya su more jin dadin kasarsu, an haddasa musu yaki da juna, an sa su sun kashe junansu a karkashin tawaye ko zanga-zangar kin jinin gwamnati. An sa su sun tarwatsa muhallansu da kansu. Sun kafa harsashen rashin jituwa a tsakaninsu, ga tabarbarewar tattalin arziki kasarsu. Sun dawo da kansu inda suka wuce, domin a maimakon ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa, yanzu ayyukan sake gina kasa ake yi. Kafin ma su samu a kafa gwamnatin da za ta maido da zaman lafiya a kasar sai an yi da gaske, domin daga nan ne takaddamar bangarori za ta faro, da masu ra’ayin rusasshiyar gwamnati da masu ra’ayin ta ’yan tawaye. Kai, a takaice dai an dai halaka wannan kasar, an maishe ta baya, an gama da ita. Ita kuwa babbar kasar da ta kai ta ga haka, za ta yi ta jin dadi na samu karin kasashen da take mallaka a karkashinta, ga shi kuma makaman da take kerawa duk ta gwada abinta, ta ga ingancinsu, ga kuma arzikin waccan kasar da yake ta kwarara a cikin taskarta.
Su kuma kananan kasashe masu tasowa, tasu kokawar ta fin karfi na wannan zamani, wanda suke yi a yanzu shi ne, nuna danniyar shugabanni ga talakawansu ta kowace irin hanya, ba dai a bari talaka ya sakata ya wala ba. Duk sun tattara dukiyar kasashensu sun kai manyan kasashe an boye musu. Sun haddasa mugun bakin talauci ga talakawansu, talaka fama da yadda zai nemi abin da zai ci shi ne kawai tunaninsa. Duk wata hanya da suka san talaka idan ya bi ta zai samu damar tunanin ’yancinsa, to sun bi ta sun kulle. Suna da hanyoyi da yawa da suke bi wurin wannan danniyar da fin karfi, kamar misali: Murdiyar zabe ga kasashen da suke siyasa, (aringizon kuri’u ga wanda aka san ba zai kai labara ba. Ka ci, ba ka ci ba kaci, yin anfani da jami’an tsaro wajen aringizo don hana talakawa katabus a kan zabinsu), cusa wa talakawa muguwar akidar siyasa da koya musu bangar siyasa, don a ba shi ’yan kudi kalilan ya sayar da ’yancinsa, tun da an san yana cikin halin tsananin rashi. Idan ko ya ankara ya fara lura da halin da yake ciki sai ya soma son ya yi bore sai a sake cusa masa wata fitinar ko a hada shi fada da kabilar da ba tasa ba, ko addinin da ba nasa ba, sai su yi ta fada da junansu, suna tashe-tashen hankula da kashe-kashe da zub da jini, daga nan sai shuwagabanninsu su ce  sun dauki matakan dawo da tsaro, sai a watsa masu jami’an tsaro, ko’ina ba walwala ba sukuni; ’yan kudin da ya kamata a yi musu aiki sai a ce an biya tsaro da su. Shi ke nan an gama da su. Idan talauci ya yi yawa sai mugun tunani ya zaburo daga nan sai mugayen ayyuka su fara yawa. Daga lokacin wannan kasa masifa ta tasa ta gaba, ba ta sake gane alkiblarta. Shi ko ’yancin dan Adam ba a sake jin duriyarsa.
To amma tambayoyinmu a nan su ne: Shin wai ina Majalisar dinkin Duniya, tare da kwamitocinta na kare ’yancin dan Adam, da na warzar da zaman lafiya da sulhu a duniya? Ina waccan manufa da dalilin tunanin da ‘Big Three’ suka yi na kirkiro ita majalisar, don hana duniya sake fadawa Yakin Duniya na Uku da kuma samarwa da tabbatar wa dan Adam ’yanci?
Dalilan wadannan tambayoyi kuwa su ne: Idan dai Majalisar dinkin Duniya tana nan kuma kwamitocinta duk suna aiki a kan tsare-tsare da manufofinta, to me ya sa tashe-tashen hankula da yake-yake da far wa juna da fin karfi da tauye ’yancin dan Adam kullum sai kara karuwa suke yi a duniya kamar wutar kara?
A da za mu iya yi wa majalisa dan uzuri, na cewa ba ta iya daukar nauyin kanta sai manyan ’ya’yanta sun tallafa mata, shi ya sa ba ta da karfi sosai kuma ba ta da cikakken harshen tsawatarwa, amma yanzu kam ba wani uzuri da za mu iya yi mata, domin yanzu mun san cewa ta tsayu da kafafunta kuma kasashenta da yawa da ba su iya taimakawa da komai a da, yanzu duk sun samu ci gaba da bayyanar sabon arziki; wanda koda za ta yi umurni da gudunmuwa a gare ta suna da arzikin da za su ba da gudunmawarsu.
To me ya sa majalisar take nuna wariya tsakanin ’ya’yanta, wasu ’yan mowa, wasu ’yan bora, wasu shafaffu da mai, wasu an bar su iska da guguwa su tafi da su? Alhali ba wata manufar da aka gina ta a kai da ta yarda da haka.
Idan muka dauki tambayarmu ta biyu, sai mu ce ko manyan kasashe biyar (Amurka, Turai, Faransa, Rasha da China) sun manta ko sun daina jaddada wa junansu wannan akida da ita ce ginshikin gina wannan majalisa? To me ya kawo haka? Amsar ke nan, halin dan Adam na son shugabanci da danniya. Amma to dan Adam ya kamata ya gane kuma ya tuna, ba abin da ya kai zaman lafiya da kwanciyar hankali dadi. Domin  ta hanyarsu ne kadai ake samun yaduwar iyali. Misali, duk inda ba a zaune lafiya, ba yadda za a yi iyali su ji sha’awar junansu balle a samu ciki, a samu haihuwa. Da za a yi nazari, duk kasar da aka dauki lokaci ana yaki cikinta, to sai an sami karancin hayayyafa kuma ga mutuwar mutane. To ka ga ’yancin da dan Adam yake da shi na yaduwar iyali ya samu babban nakasu kuma ta hanyar zaman lafiya da kwanciyar hankali ne ake samun karuwar lafiya da girma ga dan Adam, domin duk kasar da ba ta zaune lafiya, tunanin ta noma abincin da za ta ci da ’yan kasarta ba shi ne a gabanta ba. In ko ba cin isasshen abinci mai gina jiki, ba za a samu isasshiyar lafiya da ci gaban girma ba a jikin dan Adam.
Rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali yana kawo hasarar arziki da koma bayan kowace al’umma, domin da zarar babu su, ba tunanin sarrafa arzikin da ake da shi kuma kila ma makaman da ake amfani da su suka wo nakasu ga arzikin da kasar take da su, na ruwa da na karkashin kasa, kai har ma da arzikin iskar da Allah Ya azurta dan Adam da ita.
Kai hasarar da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ke jawowa ba su lissafuwa sai dai wanda ya gani. Ga uwa uba tauye wa dan Adam duk wani ’yanci da yake takama da shi a duniya.
Kuma ina son in yi wa manyan kasashen nan biyar tunasarwa da cewa, lallai su yi a hankali, kar bakin wuta ya mutu a hannunsu, domin wannan jan gwarzon aikin da manyan kasashe uku suka yi, ba karami ba ne, domin ko ba komai; sun samar da hadin kai da kwanciyar hankali da ’yanci a duniya, a zamanin su, wanda ya yi ta yaduwa, ana cin amfaninsa a duniya zuwa yau kuma duniya ta yi dadi, arziki ya bunkasa, wayewa da walwala sun yalwata. To me zai sa mu runtse idanu, mu toshe kunnuwa daga ji da ganin wannan ci gaba da aka samu a wannan karni? Me zai hana mu tashi tsaye wurin tunani da hanyoyin da za su kara wanzar da cikakken zaman lafiya a duniya?
Me zai hana majalisa ta kara wa kwamitocinta na wanzar da zaman lafiya da ’yancin dan Adam karfi da isassun kudaden da za su yadu cikin kasashenta, tun daga mataki na kasa, jiha, karamar hukuma zuwa gunduma? Domin su sami damar wanzar da manufarta, ta tabbatar da zaman lafiya da ’yancin dan Adam a kowane sako da lunguna na duniya da kuma samun damar kashe wutar fitina tun daga tushenta, a maimakon fargar-jajin da takan yi (na kai agajin abinci da magani da jami’an tsaro) idan an ce ga wata kasa can ta barke da zanga-zanga, rigima ko yaki?
A karshen muna fatar wadannan tambayoyi za su samu gamsassun amsoshi wadanda muke fatan su zama musabbabin wanzar da cikakken zaman lafiya da tsaro tare da isasshen ’yanci ga dan Adam a duniya baki daya. Amin!