’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama?
A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan […]
A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan Najeriya ’yancinsa na dan kasa, dadewarsa da zama a wuri ko kuwa jiharsa ta asali? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
A duba dadewar mutum a wuri
– Ibrahim Namakaram
Alhaji Ibrahim Namakaram Maibatir Jos: ‘’A gaskiya ya kamata a yi la’akari da dadewar mutum a wajen da yake zaune ne wajen kare ’yancinsa na dan kasa. Ba wai a ce dole sai dai dan asalin wajen da yake zaune ne a wajen ba. Domin za ka ga akwai wanda aka haife shi a wani waje kamar shekaru 80 da suka gabata. Don haka ya kamata a duba dadewar mutum a wajen da yake zaune ba tare da la’akari cewa shi bako ne a wajen ba. A yi masa komai, a ba shi dama kamar yadda za a yi wa dukkan wanda yake dan asalin wajen ne. Idan aka yi haka an kare masa ’yancinsa na dan kasa.