’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 1
A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan […]
A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan Najeriya ’yancinsa na dan kasa, dadewarsa da zama a wuri ko kuwa jiharsa ta asali? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
A yi la’akari da dadewar mutum a wuri – Salisu Ibrahim
Alhaji Salisu Ibrahim Jos: ‘’A yi la’akari da dadewar mutum a wuri ne wajen kare ’yancin dan kasa, domin idan mutum yana zaune a wuri, ya kamata a ce ya zama dan kasa a wajen, a yi masa komai ba tare da nuna masa bambanci ba. Idan ka dubi kasashen da suka ci gaba, za ka ga suna kare ’yanci da hakkokin mutanensu na ‘yan kasa a duk inda suke zaune a cikin kasashen nasu; ba tare da la’akari da cewa su ba ’yan asalin wajen da suke da zama ba ne. Za ka ga ana yi masu komai, ana ba su dama su yi komai kamar ’yan asalin wajen, ba tare da nuna masu bambanci ba. Yanzu ka ga misali kamar Shugaban kasar Amurka Barrak Obama, ba dan asalin kasar Amurka ba ne amma saboda kare ’yancin ’yan kasa irin nasu, a yanzu shi ne Shugaban kasar. Amma ka ga a nan Najeriya abin ba haka yake ba.