’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 2

A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan […]

’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 2
’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 2

A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan Najeriya ’yancinsa na dan kasa, dadewarsa da zama a wuri ko kuwa jiharsa ta asali? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Wurin zama ne abin la’akari – Mustafa Hussaini

Mustafa Hssaini: Idan  dai abin da ake cewa gaskiya ne, cewa Najeriya ta ’yan Najeriya ce, to ya dace a ce duk inda kake ya zama wajen da za ka iya wandaka da shi, domin ko wurin da ka kwashe shekaru da yawa, to ka gama sanin komai da komai na wannan wurin, domin ba wani wurin da za ka je ka samu karramawa ko mutuntawar da ya dace kamar inda aka san ka.
Kar ka manta cewa, inda aka haife ka, idan ba ka zauna wurin ba ko kuma ka saba da wurin ba, to ai kullum kai bako ne, domin idan ka ce ka bar wurin da ka dade,  ka koma mahaifarka alhali ba ka yi rayuwa a wajen ba; to ai ba wani abu da za ka iya zartarwa. Don haka, ni ina ganin inda kake zaune, ka dade, to ya zamanto cewa a ba ka damar da za a bai wa duk wani wanda ke zaune wurin, ko kuma aka haifa a wurin.”