’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 3

A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan […]

’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 3
’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 3

A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan Najeriya ’yancinsa na dan kasa, dadewarsa da zama a wuri ko kuwa jiharsa ta asali? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

A yi la’akari da jihar asali – Sharif Murtala

Sharif Murtala: “Ni a gani na, bai yiwuwa a ce garin wani ko gidan wani ya zama naka, domin komin dadin dadewa za ka koma gida kuma a can ne tushenka, domin kuwa cibiyarka na garinku ne. Kuma idan ka ce ka zama dan wata al’umma, idan ka dubi irin tsarin zamantakewar Najeriya, zai yi wuya a ce mutumin da ya dade a wuri a ce ya saje ya zama dan wannan garin; domin ko bajima ko badade idan shi bai koma gida ba sai ka ga ’ya’yansa na neman tushensu kuma da zaran sun gano sai ka ga cewa za su nemi ko dai su koma ko kuma su nemi wani abu da zai  alakanta su da ainihin mahaifar iyayensu. Saboda  haka ni ban ga dalilin da zai sa wanda zai yi wannan tunanin ba kuma a ce ya rike inda yake da zama ba ya zama wurinsa na har abada.”