’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 4

A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan […]

’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 4
’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 4

A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan Najeriya ’yancinsa na dan kasa, dadewarsa da zama a wuri ko kuwa jiharsa ta asali? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

A kula da inda mutum ya dade da zama – Bala Abubakar

Bala Abubakar Gusau: “Ya dace a bai wa mutun dama ko ’yancin zama a gari saboda dadewa a  garin, domin ai tsarin mulki ya riga ya ba da dama idan har ka shekara biyar to ka zama dan jiha, kuma kana iya neman ko wane mukami. Ai saboda irin yadda ake nuna wannan bambance-bambance ya sa kasar ma ta kasa samun zaman lafiya. Za ka sami Bayarbe ya zo Arewa ya haifi iyalansa, duk ’ya’yansa a nan ya haife su amma sai ka ji an ce ai ba dan Arewa ba ne, musamman mu ’yan Arewa sai ka samu komai dadewar ka a Kudu ba za su yarda da kai ba. Ai duk kasa daya muke, babu bambanci.”