’Yancin dan kasa: A kula da jihar asali ko wurin zama? 5
A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan […]
A halin da ake ciki, ana ta kai kawo game da ’yancin dan kasa, inda za ka ji wata jiha ta ware wasu mutane, tana kiransu da sunan baki, kawai saboda ba jihohinsu na asali ba ne. Abin tambaya a nan shi ne, shin me ya kamata a yi la’akari da shi wajen ba dan Najeriya ’yancinsa na dan kasa, dadewarsa da zama a wuri ko kuwa jiharsa ta asali? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
A kula da mazaunin mutum
– Abba Abubakar
Abba Abubakar: “Ra’ayina shi ne, ya dace a bai wa kowa ’yanci saboda da farko dai ya dace a bai wa kowa ’yancinsa na zama dan kasa kuma yana da dama na ya gudanar da sana’arsa a ko’ina. Saboda shi dan Najeriya ne, shi mutum ne mai yawo, don za ka samu dan Katsina ya tafi Aba, ka sami dan Aba ya zo Katsina. Saboda haka duk wanda ya zauna a wuri, ya kai shekara biyar to ya zama dan wannan wajen, ya dace ya ci gajiyar duk abin da ake samu a wannan wurin, don ya ci moriyar abin. Ai shi ma yana da mutanensa a wancen wajen, in dai ba za a ce kowa ya ci abin da suke da shi na albarkatunsu ba ne, kamar yadda wasu ke cewa.”