’Yancin Kai: Barau ya roƙi ’yan Najeriya su ƙauracewa zanga-zanga

Ya ce Shugaba Tinubu yana da tsare-tsare da za su ciyar da Najeriya gaba.

’Yancin Kai: Barau ya roƙi ’yan Najeriya su ƙauracewa zanga-zanga

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu haɗin kai da goyon bayan gwamnati, ta hanyar kaucewa gudanar da zanga-zanga.

Ya kuma yi kira da su kasance masu ƙasar addu’a domin samun damar inganta ƙasar.

Ya yi wannan roƙon ne cikin wani saƙo da ya fitar domin bikin cikar Najeriya shekara 64 da samun ’yancin kai, wanda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya sanya wa hannu a ranar Litinin.

Barau, ya kuma nemi waɗanda ke shirin yin zanga-zangar a ranar 1 ga Oktoba da su sauya tunani.

Ya shaida wa ’yan Najeriya cewa Shugaba Tinubu yana jajircewa wajen farfaɗo da tattalin arziƙi, magance matsalar tsaro, da kuma warware sauran ƙalubale da ƙasar ke fuskanta.

A cikin saƙonsa, Barau ya ce, “Yan uwana ’yan Najeriya, ina taya ku murnar cikar Najeriya shekara 64 da kuma samun ‘yancin kai.

’Yayin da muke bikin wannan rana mai muhimmanci, ya kamata mu tuna irin jajircewa da sadaukarwa da shugabanninmu na farko suka yi, kamar su Dokta Nnamdi Azikiwe, Cif Obafemi Awolowo, Sir Ahmadu Bello da Sir Abubakar Tafawa Balewa. Mu ci gaba da bin turbar da suka gina na haɗin kai, zaman lafiya, adalci da haƙuri.

“Ina sane da cewa muna fuskantar ƙalubale a wannan shekaru 64, amma da ikon Allah za mu shawo kan su. Mu ci gaba da tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen cimma manufofinsa da tsare-tsarensa.

“Yana da kyakkyawar niyya ga ƙasar nan, kuma za mu yi nasara.”

Barau, ya ce Majalisar Dokokin Najeriya za ta ci gaba da ƙoƙari wajen samar da kyakkyawan shugabanci, tare da tallafa wa ɓangaren zartarwa da dokoki don aiwatar da manufofinta da tsare-tsarenta.

Ya kuma ƙara da cewa, kwamitin gyaran kundin tsarin mulki da yake jagoranta yana aiki tuƙuru wajen gyara kundin tsarin mulkin ƙasar don ya dace da buƙatu da muradun ’yan Najeriya.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja