’Yancin mata a Turai da Musulunci (2)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon jiya.Ya ’yan uwa ku tuna cewa tun a karni na 5 Musulunci ya daukaka mace, daukakawar da ta kai in har mace ba ta da ra’ayin miji, to Musulunci ya ba ta damar ‘khul’i’ wato ta […]

’Yancin mata a Turai da Musulunci (2)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon jiya.
Ya ’yan uwa ku tuna cewa tun a karni na 5 Musulunci ya daukaka mace, daukakawar da ta kai in har mace ba ta da ra’ayin miji, to Musulunci ya ba ta damar ‘khul’i’ wato ta mayar masa da sadakinsa. Ku sani a lokacin jahiliyya, Larabawa sun kasance masu binne ’ya’yansu mata da ransu, sannan  duk mutumin da aka haifa masa ’ya mace yakan yi fushi, amma da Musulunci ya bayyana sai ya dakatar da duk wani nau’in wulakantawa, ya umarci  mata su dinga sa sutura domin su ma kansu sutura ne, aka umarci maza su yi tsari ga matansu domin hana su gogayya da sauran mazaje wadanda ba maharramansu ba, aka umarci mazaje su nema wa mata ’yansu da abinci da sutura da kuma karantar da su ilimin addini, idan kuma mijin ba shi da damar karantarwa ta ya kai su inda za iya karantar da su.
Ya ’yan uwana mata ku tuna cewa a Madina wani sahabi ya saki matarsa sai kuma daga baya Allah Ya jarrabe shi da sonta fiye da kima, sai ya dinga bin ta yana cewa ta yi hakuri ta dawo gare shi amma ta ki, da Manzon  Allah (SAW) ya ji labari sai ya tausaya masa ya iske matar ya ce mata ya kamata ki yi hakuri ki koma gare shi, sai ta ce ya rasullilahi shin umarni ne ko kuwa shawara ce? Sai ya ce ina dai tausaya masa ne, sai ta ce a gaskiya ya rasullilahi ba zan iya koma wa gare shi ba. Ku duba irin wannan fa?
Shin wane irin ’yanci ne Musulunci bai ba ku ba da har za ku kafa kungiyoyin kare ’yancin mata? Ku sani a Turai sai a tsakiyar karni na 20 suka samu ’yancin yin walwala da kubuta daga bauta daga hannun mazajensu, ku kuwa Musulunci ya ba ku ’yanci tun sama da shekara dubu da suka wuce, don haka ’yan uwana mata kada ku yarda da duk wata farfaganda a kan neman ’yanci, domin a zahiri Turai suna amfani da kalmar neman ’yanci ga al’ummar Musulmi domin ruguza kyakkyawar tarbiyyar Musulmi, kuma makamin da suke amfani da shi na farfaganda ya fi makamin nukiliya barna, domin zai ragargaza koyarwar addinin  Musulunci,  wanda zai sa kafin mu farga mu gyara tuni mun makara.
A karshe ina fata ’yan uwana mata za su yi hattara.
Ado Musa kaura Goje, Kano
Za a iya samunsa a wannan lambar: 08069186916

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi