Yanke farashin mai ne babban kalubalenmu – Kachikwu

Daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar Najeriya shi ne yanke farashin albarkatun man fetur, a cewar Ministan albarkatun man fetur Mista Ibe Kachikwu, inda ya jadadda bukatar da ake da ita wajen shawo kan matsalar. Da yake jawabi a wajen wnai taro na musamman da ake gudanarwa a Najeriya kan albarkatun fetur na […]

Yanke farashin mai ne babban kalubalenmu – Kachikwu

Daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar Najeriya shi ne yanke farashin albarkatun man fetur, a cewar Ministan albarkatun man fetur Mista Ibe Kachikwu, inda ya jadadda bukatar da ake da ita wajen shawo kan matsalar.

Da yake jawabi a wajen wnai taro na musamman da ake gudanarwa a Najeriya kan albarkatun fetur na duniya (NIPS) a Abuja, inda Kachikwu ya ce matukar ba a shawo kan matsalar kimanta farashin albarkatun man fetur daiskar gas ba, to gyaran matatun, tare da karfafa gwiwar masu saka jari su gina sababbi ba zai warwarematsalolin albarkatun kasar nan ba.

Ministan wanda ya gabatar da jawabi ga matsu ruwa da tsaki a wannan masana’anta mai taken “Hanyoyi bakwai masualfanu na takaitacce da matsakaicin zango da za abai wa fifiko don bunkasa masana’antar sarrafa albarkatun mn fetur da iskar gas a Najeriya,” sai dai ya ce dole a yi taktsantsan a kowane kokari da ake yi wajen nazarin kimanta farashin albarkatun man fetur, ta yadda za a tabbatar da cewa mutane ba su yi fama da wahala mara kan gado ba.

A cewarsa: “Kowa na bukatar makamashi, wato isasshen gas da man ababen hawa ba ytare da dogon layi ba, amma mutane ba a shirye suke su sadaukar da kai don ganin wadnanan al’amura sun tabbata ba.

“Sai dai, idan muka gyara matatun nan da shekara ta 20219, ko wannan na nufin mun warware matsala? A’a, ba haka lamarin yake. Za dai a ci gaba da fama da maytsalar yanke kimar farashi, saboda babu wanda zai gina matatar mai ya kuma sayar da man a asara,” inji shi.

Kuma wata matsalar da ke kara cukurkuda al’amura a cewar shugaba masu hada-hadar iskar gas a Najeriya (NGA), Injiniya Dada Thomas, wanda ya yi kira kan hadin gwiwar cin ma matsayar kimanta farashin gas da aka amince da shi ga daukacin masu saye da masu sayarwa.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno