Yankin Crimea ya zama kasa mai ‘yanci -Shugaban Rasha
A wani jawabi da Shugaban Rasha bladimir Putin ya gabatar a fadarsa da ke Kremlin a gaban masu fada a ajin kasar, ya ce yankin Crimea ya tashi daga yanki karkashin kasar Ukraine zuwa kasa mai ‘yanci da ke karkashin Tarayyar Rasha.Shugaban ya kuma kare matakin kasarsa kan yankin Crimea, inda ya ce tun da […]
A wani jawabi da Shugaban Rasha bladimir Putin ya gabatar a fadarsa da ke Kremlin a gaban masu fada a ajin kasar, ya ce yankin Crimea ya tashi daga yanki karkashin kasar Ukraine zuwa kasa mai ‘yanci da ke karkashin Tarayyar Rasha.
Shugaban ya kuma kare matakin kasarsa kan yankin Crimea, inda ya ce tun da fari shigar da Crimea cikin yankin kan iyakokin kasar Ukraine a shekarar 1954 kuskure ne. Daga nan sai ya bayyana sababbin mahukuntar Ukraine da masu kwacen iko ta hanyar juyin mulki wanda hakan ba zai taba amfanar da kasar da komai ba.
A watan da ya gabata ne dakarun Rasha suka karbe iko da yankin Crimea wanda ke cikin kasar Ukraine bayan shafe watanni ana zanga-zangar da ta tilasta wa Shugaba biktor Yanukobych sauka daga mulki. Kodayake wasu na ganin wasancewar dakarun Rasha a yanki ya taimaka wajen gudanar da kuri’ar raba-gardamar da aka kada a yankin ranar Lahadin da ta gabata inda jama’ar da ke yankin suka zabi ballewa daga Ukraine da kuri’u fiye da kashi 95 cikin dari.
Shugaba Putin dai ya ce kuri’ar raba-gardama ba ta saba wa dokokin da suka kafa kasashe ba, tun da kowace kasa tana da’yanci zabar makomarta.
Ya kuma kafa misali da ballewar kasar Kosobo daga Yugoslabia wanda ya samu goyon bayan Amurka da kawayanta, da yadda ita kanta Ukraine ta ballewa daga Tarrayar Sobiet a shekarar 1991.“Kaga ballewar yankin Crimea daga Ukraine ba sabon abu bane da zai kawo kace-nace” Inji shi
Daga bisani ya musanta zargin da Yammacin Duniya ke yi cewa dakarun Rasha sun mamaye yankin gabanin kuri’ar raba-gardamar. Inda ya ce dakarun na yankin ne kan wata yarjejeniya da Rasha ta shiga da Ukraine na wadatata da dakaru fiye dubu 25 don samar da tsaron a sansanin Black Sea Fleet da ke yankin Crimea.
Gabanin jawabinsa, shugaban ya yi watsi da takunkumin da Yammacin Duniya suka ce sun kakabawa Rasha wanda shi ne mafi tsauri tun bayan kawo karshen yakin cacar-baki. Ya ce matakin nasu ba zai sa shi ya daina wa yankin Crimea kallon‘yantartar kasa mai cin gashin kanta ba.
“Tun bayan kawo karshen yakin cacar-baki, Rasha take fuskantar takunkumi iri-iri, duk da cewa a hukumance Yammacin Duniya na ikirarin cire takunkumin tuntuni, amma a zahiri batun ba haka bane” Inji shi.
Zaman tankiya na ci gaba da karuwa tsakanin Rasha da Yammacin Duniya akan rikicin yankin Crimea, inda Amurka da Tarayyar Turai ke cigaba da daukar matakan takunkumi da kuma kwace ajiyar mahukuntar Rasha da wasu daga cikin na Ukraine masu marawa ballewar Crimea baya.
Amma Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden da Firaministan kasar Polland, Donald Tusk sun yi watsi da jawabin shugaban Rashan. “Za mu cigaba da mayar da Rasha saniyar ware kuma ba gudu ba ja da baya kan matakinmu na kakaba mata takunmi” Inji Joe Biden. Ya ci gaba da cewa Amurka za ta yi dukkan mai yuhuwa don kare muradin duk wata kasa da ke cikin kungiyar kawancan Tsaro ta NATO.
A martanin da Birtaniya ta mayar ranar Talatar da ta gabata, ta ba da umarnin dakatar da wani atisayan soji da ta shiga da Rasha. Sakataran Harkokin Wajenta William Hague ya ce ya damu matuka ganin yadda Shugaba Putin ya zabi kasancewa saniyar ware, maimakon ba ‘yan kasarsa da ma jama’ar yankin Crimea ‘yancinsu na yin mu’amala da sauran al’ummar duniya.