‘Yankin Falasdinu zai shiga kotun ICC a watan Afrilu’

Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya tabbatar da cewa yankin Falasdinu zai shiga cikin mambobin kasashen kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC a ranar daya ga watan Afrilun bana. An wallafa wannan sanarwar ce a ranar Talata a shafin intanet na majalisar, bisa yarjejeniyar kasa da kasa. Har ila yau, […]

‘Yankin Falasdinu zai shiga kotun ICC a watan Afrilu’
‘Yankin Falasdinu zai shiga kotun ICC a watan Afrilu’

Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya tabbatar da cewa yankin Falasdinu zai shiga cikin mambobin kasashen kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC a ranar daya ga watan Afrilun bana.

An wallafa wannan sanarwar ce a ranar Talata a shafin intanet na majalisar, bisa yarjejeniyar kasa da kasa. Har ila yau, samun kasancewa cikin kasashen da ke cikin kotun duniyar wata dama ce ga Falasdinawan ta gurfanar da kasar Isra’ila a gaban kotun bisa zargin aikata laifukan yaki. Sai dai su ma mayakan sa-kai na Falasdinu ka iya fuskantar shari’a.
Matakin shiga kotun ya biyo bayan bukatar da Shugaba Mahmood Abbas ya gabatar na zama cikin kasashen kotun ICC a makon jiya, wanda hakan ya tunzura Isra’ila har ta kai ga daukar dakatar da bai wa Falasdinawan kudin tafiyar da ayyukan gwamnati da suka tasamma Dala miliyan 125.
Har ila yau, a makon jiya ne Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya yi watsi da wani daftarin kudurin Falasdinawa da kasar Jordan ta gabatar wa kwamitin, wanda ya yi kira da a kawo karshen mamayar da kasar Isra’ila take yi a yankin Falasdinu nan da shekara uku. Sai dai kudurin bai samu kuri’a tara da ake bukata ba, saboda kasashe takwas ne suka aminta da shi, sannan biyar suka kaurace wa zaman ciki har da Najeriya. Kuma da Najeriyar ta goyi bayan kudurin kamar yadda aka ce Shugaba Goodluck Jonathan ya yi alkawari, da kasar Falasdinun ta samu nasara.