Yankin Kadage na bukatar abubuwan more rayuwa – Mai Unguwa Magaji

Mai Unguwar Kadage Magaji Ibrahim ya koka a kan yadda yankinsa na Kadage ke fama da karancin abubuwan more rayuwa. A kan haka ne ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da ya yi wa Allah Ya kai musu dauki cikin gaggawa. Mai Unguwar ya yi wannan kira ne a wata takardar […]

Yankin Kadage na bukatar abubuwan more rayuwa – Mai Unguwa Magaji
Yankin Kadage na bukatar abubuwan more rayuwa – Mai Unguwa Magaji

Mai Unguwar Kadage Magaji Ibrahim ya koka a kan yadda yankinsa na Kadage ke fama da karancin abubuwan more rayuwa. A kan haka ne ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da ya yi wa Allah Ya kai musu dauki cikin gaggawa.

Mai Unguwar ya yi wannan kira ne a wata takardar koke da ya aika wa jaridar Aminiya inda ya bukaci gwamnatin Kaduna da ta kawo musu dauki. Garin Kadage wanda yake karkashin karamar Hukumar Chikun yana fama da karancin abubuwan more rayuwa ne da suka hada da rashin hanyoyi masu kyau da rashin makarantu da asibitoci da tsaftataccen ruwan sha. Sauran abubuwan da ke damun yankin sun hada da rashin ofishin ’yan sanda da kuma rashin wutar lantarki. Ya ce duk garin da ya rasa wadannan abubuwa zai kasance cikin koma-baya a fannin cigaba. Ya ce gwamnatocin da suka shude sun sha yi musu alkawurra amma har yanzu shiru kake ji, don haka ne ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga wannan gwamnati mai ci da talakawa suka zabo don ta share musu hawaye.
Mai Unuwa Ibrahim ya kara da cewa, rashin wadannan abubuwa na more rayuwa ne suka kara jefa matasan yankin cikin mawuyacin hali inda da yawansu suka shiga miyagun ayyukan da suka hada da sace-sace da shaye-shaye da ma duk wadansu abubuwa marasa kyau.
Ya ce da za a samar musu da wadannan abubuwan more rayuwa ko shakka babu yankin zai bunkasa kuma za a samar da ayyukan yi ga dimbin matasan da ke zaman kashe wando. Ya ce akwai kasar noma mai kyau a yankin, amma saboda rashin kyaun hanya al’ummar da ke zaune a garin ba sa iya fitar da su zuwa wadansu garuruwa don bunkasa harkar noma. “Da yawa daga cikin abubuwan da muke noma wa sukan lalace ne saboda rashin kyawun hanyoyin,” in ji shi. Ya yi addu’ar Allah Ya samar wa Jihar Kaduna da ma kasar nan zaman lafiya mai dorewa, don a samu cigaba mai ma’ana.