Yankin ku’an Pan na fama da matsalar rashin ruwan sha
Shugaban karamar Hukumar ku’an Pan da ke Jihar Filato Mista Theophilus Dakas Shan ya ce al’ummar yankin suna fama da matsalar rashin ruwan sha mai tsabta. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a ofishinsa, inda ya ce rashin ruwan sha mai tsabta yana jefa al’ummar yankin a cikin […]
Shugaban karamar Hukumar ku’an Pan da ke Jihar Filato Mista Theophilus Dakas Shan ya ce al’ummar yankin suna fama da matsalar rashin ruwan sha mai tsabta.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a ofishinsa, inda ya ce rashin ruwan sha mai tsabta yana jefa al’ummar yankin a cikin mawuyacin hali. Mista Dakas Shan ya ce karamar hukumar tana fama da matsalar ruwan shan ne sakamakon yawan duwatsun da ake da su a yankin, wadanda suke haifar da wahala wajen haka rijiyoyi da rijiyoyin burtsatse.
Ya ce a cikin mazabu takwas da ake da su a karamar hukumar mazabu uku ne kawai ake samun ruwan sha mai tsabta a cikinsu. “Don haka ne karamar hukumar ta samar da wasu famfunan tuka-tuka da rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana, domin saukaka wahalar da al’ummar yankin suke sha wajen samun ruwan sha.
Shugaban ya ce al’ummar yankin suna fama da matsalar hanyoyin fitar da kayan amfanin gonarsu, inda ya ce wadannan matsaloli suna kawo wa yankin koma-baya a fannin tattalin arziki.