Yankunan Gashaka da Bali: Inda makafi suke noma da kamun kifi maimakon bara

A  wadansu yankunan  da ke cikin kananan hukumomin Gashaka da Bali a  jihar Taraba makafi maza da mata suna gudanar ta sanaa’ar noma da kamun kifi ne domin gudanar da rayuwarsu maimakon yin bara.Wadannan yankunan suna fama da matsalar ciwon makanta wanda wani nau’in kuda da ake kira da turanci ‘Black flies’ ke haifarwa.A wadannan […]

Yankunan Gashaka da Bali: Inda makafi suke noma da kamun kifi maimakon bara

 Waxansu daliban makarantar makafi na garin GarbabiA  wadansu yankunan  da ke cikin kananan hukumomin Gashaka da Bali a  jihar Taraba makafi maza da mata suna gudanar ta sanaa’ar noma da kamun kifi ne domin gudanar da rayuwarsu maimakon yin bara.
Wadannan yankunan suna fama da matsalar ciwon makanta wanda wani nau’in kuda da ake kira da turanci ‘Black flies’ ke haifarwa.
A wadannan yankuna akwai daruruwan makafi maza da mata  wadanda ke fama da cutar makanta kuma  duk da nakasar da suke da ita na rashin ido suna iya gudanar da ayyukan noma da kamun kifi.
A karamar hukumar Gashaka wakilinmu ya sadu da makafi masu yawan gaske a garin Garbabi, inda nan ne aka fi samun yawan makafi a yankin na karamar hukumar Gashaka.
 Hakimin gundumar Garbabi, Alhaji Sale Umaru ya ce, matsalar cutar makanta ta addabi al’ummarsa kuma ta hana su sakat. A cewarsa, akwai maza da mata masu yawan gaske wadanda suka makance a sanadiyar wannan cuta, wanda wani nau’i na kuda ke haifarwa.
Yace, an shafe sama da shekaru hamsun ana fama da wannan cutar a yankin na Garbabi da na Dakkah a karamar hukumar Bali.
Alhaji Sale Umaru  ya kara da cewa, an soma samun dauki daga gwamnati ta hanyar bai wa masu cutar wani magani mai suna ‘Mactizan’ wanda ake hadiya a shekara-shekara kuma yana rage kaifin  cutar.
Ya ce, akwai kauyuka sama da goma sha uku inda wannan  cuta ta yi wa jama’a illa. kauyukan a cewarsa, sun hada da Barmai da Waya da Mude da Kabarin Bature da kuma Shinna. Sai kuma Mawanka da Gayam da Maisunma da Kunkai daMakulkano da Jauro jalo da Kwar da kuma Garbadbi
Wata mata wadda ta  makance a sanadiyar wannan cuta, mai sunaRakiya Yakubu, ta shaida  wa wakilinmu cewa, ta  makance ne bayan shekaru takwas da yin   aurenta  a wani kauye . Ta ce tana gona tare da mijinta suna noma  sai zazzabi ya buge ta, wanda haka din ya sanya  ta koma gida. Ta  ce tayi fama da zazzabi na watanni kuma daga karshe ta makance, domin ba a kai ta asibiti ba.
 Ta kara da cewa, duk da kasancewarta makauniya har yanzu tana yin noma, domin ba ta da wata sana’a.
Wani makaho mai suna Hamidu Garba, ya bayyana cewa, kafin ya makance shekaru talatun da suka wuce, shi dalibi ne a makarantar gwamnati da ke garin Bali.Ya ce a lokacin hotu ne yay i rashin lafiya daga nan kuma ya makance, wanda hakan ya sa  ya   bar makanta.
A cewar,sa yanzu noma yake yi, duk da kasancewarsa  makaho,  ya kara da cewa, akwai makafi masu yawan gaske a yankin wadanda suke gudanar da sana’o’in noma da kama kifi. “Yawancinmu a nan mun fi son mu yi sana’a  a maimakon bara, “inji Hamidu Garba.
 Ya kara da cewa, akwai bukatar gwamnati ta samar da wuraren koyar da sana’o’i  ga makafi don su dogara da kansu a maimakon yin bara.
A yankin na Garbabi gwamnatin jihar Taraba ta gina  makarantar sakandare ta makafi yara maza da mata. A cewar hakimin gundumar Garbabi, an gina makarantar ne don a bai wa yara wadanda ke fama da makanta  ilmin zamani. Ya ce wannan ya sa iyayen yara makafi daga sassa daban-daban na jihar,  har ma daga wajen jihar  mutane na turo ‘ya’yansu zuwa wannan makaranta.
A makarantar makafin da ke kan hanyar Bali zuwa Gembu, akwai sama da dalibai dari da talatin, maza da mata.
Shugaban makarantar, wadda ita ma makauniya ce, mai suna  Madam Grace Dubu Tankwa, ta shaida wa wakilinmu cewa, tun tana ‘yar shekara goma ta  makance.Ta ce ciwon bakondauro ne ya zama sanadiyar makantarta, amma ta  ce  tayi sa’a, domin iyayenta sun sanya ta a makaranta har ma ta samu digiri.
Ta ce akwai dalibai sama da tari da talatin a makarantar, kuma daliban sun kasance maza  da mata. Ana koyar da su darursan turanci da lissafi da kimiyya da fasaha, kuma daliban duk da kasancewarsu makafi suna nuna kwazo da himma wajen karatu.
Madam  Grace ta kuma yi tsokaci kan yadda wadansu  iyayen yara  ke kin tura yaransu makafi makaranta a yankin, duk da kasancewar akwai yara maza da mata masu  makanta a yankin.
Ta ce bai wa nakasasu ilmi abu ne mai mahimmanci domin zai taimaka wa irin wadannan yara samun madogara mai kyau idan sun girma.
Shugaban makarantar ta kara da cewa, akwai bukatar gwamnatin jihar  ta samar wa makarantar kayan koyarwa na zamani tare  da  motar jigilar  dalibai da kuma dakin shan magani.
Da yake magana dangane da wannan cutar, wani kwararen likita mai suna Dokta Inusa Dakkah, wanda dan  asalin yankin Dakkah  da ke karamar hukumar Bali  ne, yankin da ke fama da wannan cutar  ta makanta, ya ce wani nau’in kuda ne yake haifar da cutar.
A cewarsa, wannan kudan idan ya ciji mutum yana zuba wata tsutsa wanda ke shiga jinin mutum ta lalata jijiyoyin ido. Ya ce wannan cutar tana zama a jikin dan  Adam har na tsawon watanni goma sha bakwai zuwa shekaru goma sha bakwai kafin su haifar da makanta.
Ya ce wannan cuta tana haifar da  illa ga daukacin al’ummar yankin Dakkah  kuma duk wanda ke zaune a yankunan da ke da  kogi mai  ruwa da ke gudu  sosai yana iya kamuwa da wannan cutar.
Dokta Inusa Dakkah ya kara da cewa, irin wannan kudaje da ake kira “black flies’ sun fi rayuwa a cikin kogunan da ruwansu ke gudu  sosai,   watau kamar  kogin Taraba, wanda asalinsa daga tsaunin Mambila ne.
Ya ce har yanzu ba a samu rigakafin cutar ba, kuma tana kama yaro da babba. Ya ce a kasar nan yankunan  kananan hukumomin Gashaka Da Bali ne cutar ta fi  yawa.