Yanzu ba a sayen mutane a siyasa – Mace ’yar takarar Gwamna

Sanata A’isha Jummai Alhassan Sanata ce daga Jihar Taraba, kuma a halin yanzu ita ce mace ’yar takarar Gwamna a Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC. A wannan tattaunawa da ta yi da Aminiya ta yi bayanin dangantakarta da dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC Janar Buhari da kuma dambarwar siyasar da ke gudana […]

Yanzu ba a sayen mutane a siyasa – Mace ’yar takarar Gwamna

Sanata A’isha Jummai AlhassanSanata A’isha Jummai Alhassan Sanata ce daga Jihar Taraba, kuma a halin yanzu ita ce mace ’yar takarar Gwamna a Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC. A wannan tattaunawa da ta yi da Aminiya ta yi bayanin dangantakarta da dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC Janar Buhari da kuma dambarwar siyasar da ke gudana a Jihar Taraba. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ana rade-radin cewa akwai rashin jituwa tsakaninki da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, mene ne gaskiyar wannan lamari?
A’isha Alhassan: Wannan ba gaskiya ba ne, akwai kyakkyawar fahimta tsakanina da Janar Muhammadu Buhari, domin duk lokacin da na hadu shi nakan durkusa in gaishe shi. Bari in fada maka, duk lokacin da shi Janar ya gan ni abin da yake fara kirana da shi shi ne “Gwamnata,” kafin ma mu soma gaisuwa. Ni kuma sai in ce lafiya lau Sa, saboda haka akwai kyakkyawar fahimta tsakanina da Janar Buhari.
Kuma siyasa ba yaki ba ne ko kuma abin gaba, duk da kasancewar ban yi shi ba a lokacin zaben fidda dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyarmu ta APC da aka gudanar a garin Legas, amma Janar Buhari bayan mun dawo daga Legas ya tafi gidan dan takarana Alhaji Atiku Abubakar a Abuja ya gode masa ya kuma nemi hadin kansa. Ni ba ni da wani abu a zuciyata,  wato ba ni da wata kullaliiya ko gaba da Janar Muhammadu Buhari. A zaben shekarar 2011 ina cikin Jam’iyyar PDP, amma Janar Buhari na zaba, saboda wani dalili na kashin kaina.
Aminiya: To me ya kawo wannan zargin?
A’isha Alhassan: Wannan aikin jahilan ’yan siyana ne wadanda ke yin gaba da wadanda ba su zabi wani dan takara ba. In ban da jahilci,  ya kamata a ce daga ranar da aka zabi  Janar Buhari a matsayin dan takarar Shugaban kasa, to a ce babu sauran maganar ofishin kamfen na Janar Buhari.
Abin da ya kamata shi ne, a maida hankali wajen gudanar da kamfen don ganin Janar Muhammadu Buhari ya samu nasara, ba wai ka-ce-na-ce ba, kamar abun da ke faruwa a Jihar Taraba. Saboda haka idan su jahilan ’yan siyasa ne shi Janar Buhari ba jahilin dan siyasa ba ne.Kuma ya kamata jama’a su san matsayina a kan Janar Muhammadu Buhari, shi uba ne a gare ni, kuma shi ne dan takarar Shugaban kasa na jamiyyarmu. Zan bayar da gudunmawata ga kamfen dinsa domin ganin Janar Buhari ya lashe zabe saboda in kara jaddada cewa ba ni da wata matsala da Janar Buhari, yana goyon bayana, ni kuma ina goyon bayansa.
Aminiya:  Wasu mutanen ofishin kamfen na Janar Buhari a Jihar Taraba sun ce ba a yi zaben gaskiya ba a lokacin da aka zabe ki a matsayin ’yar takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a jihar. Me za ki ce?
A’isha Alhassa: Idan za a yi zaben fidda da dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Taraba sau dari zan lashe zaben. Duk wanda ya kasance a inda aka gudanar da zaben fidda dan takarar Gwamna na jam’iyyarmu ta APC a Jalingo ya san cewa zabe ne na gaskiya aka yi, ba wai dauki dora ba, babu wani magudi, ko faifan bidiyo na zaben yana nan, saboda haka ba a boye aka yi wannan zabe ba.
Kamar yadda kowa ya sani, kowane wakili ya kada kuri’arsa a lokacin zaben , wadanda suka fadi zabe ne suke irin wadannan maganganu marasa tushe domin su kawo rudani a tafiyar da muke yi. Ya kamata irin wadannan mutane su sani cewa yanzu an daina siyasar kudi. Wadannan ’yan takara da ba su yi nasara ba, ba sa tare da jama’a. Sun dade ba su zo Jihar Taraba ba, sai kawai da zabe ya karato suka shigo Taraba, akwai wani dan takara ma kwana hudu kacal ya rage a yi zabe ya shigo garin Jalingo.
Yanzu ba a sayen mutane a siyasa, mutane suna tare da wanda yake tare da su ne, ba wai kawai sai lokacin zabe mutum ya dauko kudi ya ce yana neman ya sayi jama’a ba. Abin da ya kamata wadannan ’yan siyasa su yi shi ne su natsu su gano inda suka yi kuskure su gyara don gaba. Amma sun kasa yin haka sai surutan banza. Ina kara nanata cewa idan za a yi zaben fidda ’yan takara sau dari zan yi nasara, domin ina tare da mutane, mutane suna tare da ni.
Wadansu daga cikin wadanda suka fadi zabe sun raba kudi, amma an ki zabensu, daga cikinsu akwai wadanda suka bayar da Naira dubu talatin da biyar, wadansu kuma sun bayar da Naira dubu ashirin da biyar, amma an ki zaben su domin ba sa tare da jama’a.
Aminiya:  Ana zargin cewa kafarki daya na cikin Jam’iyyar APC ne daya kuma na cikin Jam’iyyar PDP, haka ne?
A’isha Alhassan: Ana yin wannan zargin ne don na je taryar Alhaji Sani Abubakar danladi a lokacin da ya iso Jalingo bayan Kotun koli ta bayar da umurnin cewa a maida shi kan mukaminsa. Tun kafin a tube shi akwai kyakkyawar dangantaka  tsakanina da shi, kuma a da can a Jam’iyyar PDP muke, sannan a lokacin da na tsaya takarar Sanata na mazabar  Taraba ta Tsakiya ya taimaka mini na ci zabe.
Abu na biyu shi ne, daya daga cikin dalilan da danbaba Suntai ya kawo don a tsige Alhaji Sani danladi shi ne, wai ni da shi da Sanata Tutare Abubakar  mun hadu mun kitsa yadda za mu kashe shi danbaba Suntai a lokacin da muka tafi aiki Umara a kasar Saudiyya. A zahirin gaskiya ba mu hadu da Sani danladi a kasar Saudiyya ba, domin a ranar da na bar kasar Saudiyya a ranar ce shi kuma Sani danladi ya isa kasar.
To, ganin dukkan dalilan da aka bayar a matsayin hujjar cire Alhaji Sani danladi duk karya ne, sai na kira ’yan majalisar Jihar Taraba daya da daya na ba su shawarar cewa wannan abin da suke so su yi, ba gaskiya ba ne, kuma zai iya kawo rigima a jihar, amma suka ki jin shawarata. Kowa ya san cewa ba a bi gaskiya ba wajan tsige Alhaji Sani Abubakar danladi.
Bayan wannan kuma lokacin da ya yi gudun hijira ya zo Abuja, yakan zo ya gaida da ni, ni ban kashe ko kwabo a wajen shari’arsa ba, amma na taya shi addu’a wajen ganin Allah Ya taimake shi ya samu hakkinsa da aka tauye ta hanyar tsige shi da aka yi ba a kan ka’ida ba.
Sannan kuma ya kamata ka fahimce cewa an yi haka ne don wanda aka tsige a kan mukaminsa a shafa masa kashin kaji a hana shi ya tsaya takara har sai bayan shekara goma.
Kamar yadda na fadi tun farko cewa akwai fahimta kyakkyawa a tsakanina da shi, saboda haka ashe bai zama laifi ba, idan na taya wannan mutum murna bayan ya samu nasara a kotu.
Ya kamata kowa ya san cewa, in don na je taryar Alhaji Sani danladi shi ne laifi, to na yi laifin kuma Alhaji Sani danladi ya dawo Jihar Taraba a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, kuma ni Sanata ce wadda ke wakiltar mahaifarsa, saboda haka ban ga wani laifin yin haka ba.