Yanzu burodi da wake sun gagare mu — Leburori
A yanzu ko ’yan mata masu sayar da faten wake sun daina yawon tallansa sabanin yadda suke yi a baya.
Leburori a Jihar Taraba sun koka kan yadda saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a yanzu hatta burodi da wake sun gagare su ci.
Galibin leburorin da Aminiya ta zanta da su sun bayyana cewa sun manta yaushe rabonsu da cin burodi da wake saboda yanayin tsadar rayuwa da aka tsinci kai a ciki.
Wasu daga cikin leburorin sun bayyana cewa abin da suke samu a rana na kuɗin sallama ba ya isa su ciyar da iyalansu ballantana sauran larurorin yau da kullum.
Wani birkila mai suna Dauda Maidawa, ya shaida wa Aminiya cewa yana samun aƙalla N4000 zuwa N5000 a rana, amma kuɗin ba zai isa sayen awo uku na garin tuwo ko na kwaki ba wanda su ne mafi araha a yanzu.
A cewarsa, yanzu burodi da wake sun yi tsadar da ta gagari talaka, yana mai cewa burodin naira ɗari biyar girmansa bai taka kara ya karya ba.
“A yanzu ko ’yan mata masu sayar da dafaffen wake sun daina yawon tallansa sabanin yadda muka saba gani a baya suna kawo mana saboda yanzu awon wake ya kai N5,000 zuwa N6,000.
Ya ce abincin da ya fi shahara a tsakanin leburori bai wuce Kunun Zaƙi da Awara ba.
Sai dai su ma masu gidajen burodi sun alaƙanta tsadar burodin da tashin farashin fulawa, sukari da icce da tsadar kuɗin sufuri.
Wani mai gidan burodi a Jalingo, Haruna Adamu, ya ce a ’yan watannin da suka gabata, buhun sukari mai nauyin kilo 50 bai wuce N50,000 ba, amma a yanzu farashinsa ya kai N90,000.
Haka kuma, ya ce farashin buhun fulawa mai nauyin kilo 50 da a watannin baya suke saye N36,000, a yanzu ta koma N70,000 yayin da kuma jarkar man gyaɗa mai nauyin lita 25 da suke saye N25,000 yanzu ta koma N37,000 zuwa N40,000.
Kazalika, Haruna Adamu ya ce farashin duk wasu sunadarai da suke amfani da su wajen gashin burodi sun yi tsadar da dole su ma su ƙara farashi.
Shi ma wani mai gidan burodi mai suna Victor James da Aminiya ta zanta da shi, ya ce dole ne farashin burodi ya ci gaba da tashi saboda duk wasu kayan haɗa burodin kama daga fulawa, sukari da mai sun yi tsadar gaske.
Ya ce a bara kaɗai sau uku suna ƙara farashin burodi, lamarin da ya sa wasu suke haƙura da sana’ar yayin da mafi rinjayen kaso na masu sayen burodin sun haƙura da cinsa.