Yanzu da Shugaba Buhari ya nada Ministoci
Ina fata cikin yardar Allah zuwa lokacin da mai karatu ke karanta wannan makala Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kuma tura sababbin ministocinsa zuwa ma’aikatu daban-daban, don su kama masa a ayyukan da ya yi wa ’yan kasa alkawarin aiwatarwa a wannan zangon nasa na karshe, wato zuwa ranar 29 ga Mayun 2023, […]
Ina fata cikin yardar Allah zuwa lokacin da mai karatu ke karanta wannan makala Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kuma tura sababbin ministocinsa zuwa ma’aikatu daban-daban, don su kama masa a ayyukan da ya yi wa ’yan kasa alkawarin aiwatarwa a wannan zangon nasa na karshe, wato zuwa ranar 29 ga Mayun 2023, in Allah Ya kai rai.
Samuwar haka ba ya rasa nasaba da yadda Majalisar Dattawa cikin nuna kishin kasa da sadaukarwa ta ki tafiya hutunta na shekara, kuma cikin zaman yini biyar, wato Laraba 24 da Alhamis 25 da Juma’a 26 da Litinin 29 da kuma Talata 30, ga Yulin da ya gabata ta tantance sunayen tsofaffi da sababbin ministocin da a wannan karo suka kai 43. Sabanin shekarar 2015, mai ministoci 36 daya daga kowace jiha. A wannan karo ma dai babu matasa a jerin sunayen ministocin.
Amma Shugaban Kasar ya cika alkawarin da ya yi na zai kara yawan ministoci, bisa ga kara kirkiro sababbin ma’aikatu da zai yi.
Jihohi bakwai da suka hada da Edo da Kano da Bauchi da Kwara da Legas da Anambra da Kaduna su suka samu ministoci bibbiyu, karin da Shugaban yake da ikon yi daidai yadda yake ganin kowace jiha ta taimaka masa, ko ma bisa ga radin kansa.
Sababbin ministocin a wannan karo sun hada da tsofaffin gwamnonin jihohi takwas da sanatoci bakwai, masu ci yanzu ko wadanda suka taba danawa.
Daga cikin tsofaffin ministoci 36 da Shugaba Buhari ya yi zangon farko da su, 14, daga cikinsu sun samu dawowa, ko dai a kan gamsuwa da irin kwazon da suka nuna a zangon farko ko a bisa amincewar da ya yi musu a zaman makusantansa na tsawon lokaci, kamar yadda masu kula da harkokin siyasar kasar nan suke fassara dawowar tasu. Ma’ana ba lallai ba ne don sun taka wata muhimmiyar rawar a ji a karas. Sun ko hada da Hajiya Zainab Ahmed tsohuwar Ministar Kudi daga Jihar Kaduna wadda ita kadai ce ta dawo a cikin mata biyu da suka saura a gwamnatin daga cikin mata shida da aka fara gwamnatin Buhari da su. (Hajiya A’isha Abubakar daga Sakkwato da ta saura ba ta komo ba) Sauran hudun sauka suka rika yi a hankali.
Ana sa ran wadansu tsofaffin ministocin su koma ma’aikatunsu, don ci gaba da ayyukan da suka fara aiwatarwa. Wadansu daga cikin ministocin da za su sake danawa bayan Hajiya Zainab, akwai Dokta Chris Ngige tsohon Ministin Kwadago da Ingancin Aiki da Malam Adamu Adamu na Ma’aikatar Ilimi da Dokta Ogbonnayo Onu na Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Alhaji Muhammad Musa Bello na Babban Birnin Tarayya, Abuja da Sanata Hadi Sirika na Ma’aikatar Harkokin Jiragen Sama da Cif Rotimi Amaechi na Ma’aikatar Sufuri da Alhaji Babatunde Fashola na Ma’aikatar Wutar Lantarki da Ayyuka da Gidaje da Injiniya Sulaiman Adamu na Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da na Shari’a Babban Lauya Abubakar Malami da na Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed.
Wadansu daga cikin sababbin ministocin sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Osun Alhaji Rauf Aregbesola da Mista Geoffrey Onyeama da Alhaji Maigari Dingyadi da Hajiya Sadiya Umar Farouk da Birgediya Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) da Alhaji Mohammed H. Abdullahi da Hajiya Ramatu Tijjani da Alhaji Sabo Nanono da Madam Paulen Tallen da Sanata George Akume da Mista Festus Keyamo da Madam Gbemisola Saraki da Malam Ali Isa Pantami da Uwargida Sharon Ikeazor da Sale Mamman da Mista Goddy Jedy Agba da Mista Clement Ike.
A gefe daya kuma Majalisar Dattawa ta amince da bukatar da Shugaba Buhari ya gabatar mata na ta amince masa ya nada masu ba shi shawara na musamman mutum 15.
Ka iya cewa da samun wannan amincewa ta ministoci da mashawarta na musamman da Majalisar Dattawa ta yi wa Shugaban Kasa, abokan aiki sun samu ga gwamnatin APC. Sun kuma samu a cikin lokacin da ya dace, wata biyu da hawan Shugaban Kasa karagar mulki a karo na biyu, sabanin karo na farko da Shugaba Buhari ya yi ta nuku-nuku har aka kwashe wata shida babu ministocin. Jan kafar da masana tattalin arzikin kasa suka ce ya yi matukar taimakawa wajen kawo tawayar tafiyar da gwamnati, musamman a kan samar da ayyukan raya kasa.
Saura da me? Tunda yanzu dukkan abokan aikin da Shugaba Buhari ke bukata sun samu, yanzu ’yan kasa, musamman na jihohin Arewa da suke ta kokawa a kan a wa’adin farko duk da suke kan gaba wajen yi wa Shugaba Buhari ruwan kuri’u, amma bayan cin yakin, sai aka bar su da kuturun bawa. Ma’ana ba su gani a kasa ba a kan sharbar romon dimokuradiyya, idan aka kwatanta da ayyukan raya kasa irin na gina hanyoyin mota da na jirgin kasa da makamantansu da gwamnatin ta himmatu wajen yi wa takwarorinsu na jihohin Kudancin kasar nan, musamman shiyyar Kudu maso Yamma ta ’yan kabiyar Yarbawa.
A wannan karon ma, ’yan Arewa na ganin su ke kan gaba wajen kada wa Shugaba Buhari zunzurutun kuri’a, don haka suke fata kada shi Buhari ya sake maimaita ’yar gidan jiya gare su.
A wani bangaren tun farko ka iya aza laifin rashin samun ayyukan raya kasar a kan mutanen Arewan. Abin da ya sa na ce haka a gangamin neman kuri’a a zaben shekarar 2015, da shugaba Buhari ya kawo Kano, Kanon da har gobe ita ce cibiyar kasuwanci da masana’antu da ma sauran hada-hadar tattalin arziki a jihohin Arewa baki daya, ya gana da ’yan kasuwa da masu masana’antu da ma shugabannin kungiyoyinsu da sauran masu ruwa-da-tsaki a fannoni daban-daban, amma abin mamaki, ba wani mutum da sunan shi kansa ko wata kungiya da ya gabatar wa ayarin Shugaban Kasar wata rubutacciyar bukata kan yadda za a inganta fannin kasuwanci ko na masana’antu a Kano. Dukkan wadanda suka samu damar yin jawabi da ka suka yi, har ta kai Daraktan Yakin Zaben wancan lokaci Cif Rotimi Amaechi ya ce lokaci ya kure musu, za su wuce, duk mai wata kasida ya aiko da ita, abin da har zuwa wannan lokaci ba wanda ya mika bukatar hakan, koda ta layi daya. Alhali da aka je Legas da Fatakwal da Enugu a rubuce jama’a da kungiyoyi suka mika wa Shugaba Buhari bukatunsu. Hakan ya sa yanzu mutanen Arewa suka zama ’yan kallo a kan ayyukan raya kasar da gwamnatin Shugaba Buhari take gudanarwa a Kudancin kasar nan.
Saura da me? Yanzu ya zama wajibi, Shugaban Kasa da ministoci da gwamnoni da wakilan majalisun dokoki na kasa da duk wani mai rike da mukami a wannan gwamnati daga Arewa, su mike tsaye su yi tsayin daka wajen ganin me Arewa za ta samu a ayyukan raya kasa daga Gwamnatin Tarayya a wannan zango da shi ne na karshe a Jam’iyyar APC da dan Arewa zai yi mulki, sai kuma in da rai da rabo dama ta sake zagayowa.