Yanzu farashin batiran mota ya fadi kasa – Ibrahim Namakaram

Wani dan kasuwa da yake gudanar da harkokin  sayar da batiran mota sababbi da tsofaffi, a garin Jos babban birnin Jihar Filato Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana cewa yanzu farashin batiran mota ya fadi kasa, da kamar kashi daya bisa uku. Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar […]

Yanzu farashin batiran mota ya fadi kasa – Ibrahim Namakaram

Wani dan kasuwa da yake gudanar da harkokin  sayar da batiran mota sababbi da tsofaffi, a garin Jos babban birnin Jihar Filato Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana cewa yanzu farashin batiran mota ya fadi kasa, da kamar kashi daya bisa uku.

Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos.

Ya ce gaskiya yanzu akwai baban kalubale kan harkokin kasuwancin sayar da batiran mota, domin yanzu farashin batiran mota ya fadi kasa.

Alhaji Ibrahim Namakaram ya yi bayanin cewa misali kamar farashin sabon batirin da ake sayarwa  ada kan kudi  naira dubu 23, yanzu ya dawo naira dubu 16.   Haka kuma batirin da ake sayarwa ada kan kudi naira  dubu 20 yanzu ya dawo naira  dubu 14.

Har’ila yau ya ce kamar babban batirin da ake sayarwa ada kan naira dubu 40, yanzu ya  dawo naira dubu 33. Haka kuma batirin da ake sayarwa ada kan naira  dubu 50, yanzu ya dawo dubu 40, zuwa naira  dubu 42.

Alhaji Ibrahim ya ce babban dalilin da ya kawo faduwar farashin batiran mota shi ne, yanzu kamfanonin batira sun yi yawa a duniya. Don haka akwai gasa tsakanin wadannan kamfanoni da suke yin batura.

Ya ce  a kullum wadannan kamfanoni suna turo da wadannan batira, don haka suka cushe farashinsu ya fadi kasa.

‘’Haka suma matattun batira da ada muke saya a cika mana, mu bayar da sabo  yanzu farashinsu ya karye, saboda yanayin  harajin da ake biya wajen fita da irin wadannan tsofaffin batira zuwa kasashen waje, don kai wa kamfanonin da suke sarrafasu. Masu fita da irin wadannan tsofaffin batira, suna samun matsala wajen biyan kudaden haraji, domin ‘yar ribar da suke samu duk tana tafiya ne wajen biyan kudaden haraji’’.