Yanzu kasashen duniya sun fara goya mana baya – Jakadan Falasdinu a Najeriya
Yanzu kasashen duniya sun fara goya mana baya – Jakadan Falasdin a Najeriya
Jakadan kasar Falasdinu a Najeriya, Abdullah Shawesh ya yaba da karuwar fahimta da goyon baya da ya ce a yanzu al’ummar duniya ta nuna musu kan mamayar da kasarsa ke fuskanta daga Isra’ila da kuma mayar da al’ummarta ’yan gudun hijira.
Ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da wasu ’yan jarida da ofishin jakadancin kasar da ke Abuja a ranar Laraba.
- Yadda aka kashe Janar Alkali a Jos – Mai bayar da shaida a kotu
- Jarumin fiM din ‘The Transporter’ ya bayyana goyon bayansa ga Falasdinawa
A cewar Jakadan, hakan na faruwa ne duk da farfaganda da goyawa kasar Isra’ila baya da yawancin kafofin watsa labarai na kasashen yammai ke yi.
Abdullah ya kuma yi alla-wadai da yadda wasu shugabannin kasashe ke rububin kai ziyara tare da ayyana goyon bayansu ga kisan kare-dangin da a ke yi wa al’ummar Faladinawa, baya ga taimakawa da su ke yi a lamarin ta fuskar kayan yaki.
Ya ce, “Mun yi alla-wadai da kamfe na batanci da kasar Isra’ila ta kaddamar tare da abokan huldarta na kasashen yamma kan Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres don kawai ya fito ya yi bayani kan hakikanin abin da ke faruwa a Zirin Gaza.
“Hakan ya yi daidai da manufar kasar ta neman rufe bakin kowa tare da hali na tirsasawa da kuma aikata ta’addanci kan duk wani da ya bukaci yin amfani da dokar duniya kan hakkokin al’umma,” in jin shi.
Jakadan, wanda ya ce alhakin ’yan jarida ne su ba da labari kan hakikanin abin da ke faruwa, sai dai ya ce a zahiri yawancin kafofin watsa labari na kasashen yamma na matsayin ’yan amshin shata ne kawai wajen watsa manufofin gwamnatin masu yi masu mamayar.
“Wannan kira ne na neman a farka daga barci musamman da yakar zalunci da a ke yi wa al’ummar Falasdinawa da ke matsayin mulkin mallaka da kasashe irin naku suka fuskanta a baya,” in ji Jakadan.