Yanzu kotunan kararrakin zabe na kwatanta adalci – Barista B.K. Adam

Wani lauya mai zaman kansa da ke zaune a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, Barista B. K. Adam ya bayyana cewa, yanzu kotunan sauraron kararrakin zabe da ke zama don sauraron kararrakin zabubbukan da suka gabata, suna  kwatanta adalci. Barista B.K. Adam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.Ya ce […]

Yanzu kotunan kararrakin zabe na kwatanta adalci – Barista B.K. Adam
Yanzu kotunan kararrakin zabe na kwatanta adalci – Barista B.K. Adam

Wani lauya mai zaman kansa da ke zaune a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, Barista B. K. Adam ya bayyana cewa, yanzu kotunan sauraron kararrakin zabe da ke zama don sauraron kararrakin zabubbukan da suka gabata, suna  kwatanta adalci. Barista B.K. Adam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce hukunce-hukuncen  da wadannan  kotuna ke yankewa a yanzu ya saba  da yadda irin wadannan kotuna suka rika yankewa ada.
“A baya da wuya kaji an ce an kwace zabe a hanun gwamna ko da  ya ci zabe ta hanyar da ta dace, ko  ta hanyar da ba ta dace ba.  Amma yanzu ga shi  wadannan kotuna suna ayyukansu kamar yadda ya kamata. Don haka an samu canji kan yadda ake yanke hukumci a wadannan kotuna.”
Barista B.K. Adam ya yi bayanin cewa  gaskiya yanzu an samu canji a bangaren kotuna a kasar nan baki daya.  Domin  a baya kotuna da alkalan kasar nan, sun kasance hannayensu a daure, saboda tsoma bakin da ake yi musu,  sakamakon rashin kyakkyawan shugabancin da ake da shi a kasar a baya.
Ya ce misali kamar hukumomin EFCC da ICPC da hukumar da’ar ma’aikata ta kasa duk wadannan hukumomin doka ce ta kafa su, kan su yaki cin hanci da rashawa  a kasar nan, amma ada ba a jin duriyarsu. Saboda rashin kyakkyawan  shugabancin da muke da shi da a kasar nan.
Ya ce amma wannan sabuwar gwamnati da ta zo, tace ita  za ta yi yaki da cin hanci a kasar nan. Kuma  ta ce ba za su tsoma baki kan maganar hukunce-hukuncen kotuna da maganar  yaki da cin hanci  a kasar nan ba.
“Wannan mataki da wannan sabuwar gwamnati ta dauka shi ne ya karfafa wa kotuna da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa gwiwa kan ayyukansu. Babu shakka wannan mataki da wannan gwamnati ta dauka ya kara wa Najeriya mutunci a idanun duniya,’’ inji shi.
Ya yi kira ga  al’ummar kasar nan kan su guji sanya son zuciya kan hukunce-hukuncen da kotuna suke yankewa a kasar nan.
A cewarsa: “Mu rika kallon irin wadannan hukunce-hukunce da adalci, mu karfafa wa kotuna gwiwa domin su cigaba da gudanar da ayyukansu. Su kuma  kotuna da alkalai da lauyoyi  subi doka da oda, idan muka yi haka zamu cimma nasara.”