Yanzu mata za su iya fara cin gadon mahaifansu a Akwa Ibom – Kotu

A baya dai ‘ya’ya mata ba su da ‘yancin cin gadon mahaifansu

Yanzu mata za su iya fara cin gadon mahaifansu a Akwa Ibom – Kotu

Uba da ‘yarsa

Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Uyo, babban birnin Jihar, ta tabbatar da cewa ’ya’ya mata na da damar cin gadon mahaifansu maza idan suka mutu.

Kotun ta kuma umarci wani mutum mai suna Sampson Silas Udoh da ya ba wasu ’ya’yan dan uwansa da ya rasu Naira miliyan 20, wanda a baya ya hana su cin gadon shi.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Ntong Ntong, ya umarci mutumin da ya biya yaran diyyar ne saboda ya danne musu hakki da kuma ’yancin da doka ta ba su na cin gadon mahaifinsu.

An dai shigar da karar ce tun ranar 16 ga watan Agustan 2022.

Alkalin ya bayyana abin da mutumin ya yi da cewa take hakki ne da kuma nun rashin adalci da danniya, inda ya ce matakin mutumin ba shi da wata madogara a doka.

“Babban abin da masu karar suka nema shi ne a tabbatar musu da ’yancinsu na ikon cin gado, sabanin yadda dan uwan mahaifinsu ya danne musu, saboda su mata ne,” in ji alkalin.

Daga nan sai alkalin ya jawo hankalin dukkan masu rike da sarautun gargajiya a Jihar da cewa lokaci ya yi da ya kamata su san cewa ’ya’ya mata ma na da damar cin gadon mahaifansu kamar takwarorinsu maza.

“Ba zai yiwu a kyale wanda ake kara ya yi amfani da raunin wadannan yaran ba, don kawai su mata ba ne ya danne musu hakkinsu,” in ji Mai Shari’a Ntong.

Har yanzu al’ummomi da dama a jihar ta Akwa Ibom da ma wasu sassan Kudancin Najeriya na hana ’ya’ay mata cin gadon mahaifansu idan suka mutu, saboda yanayin al’adunsu da suka hana mata cin gado.