‘Yanzu muka san ana dimokuradiyyar gaskiya’

Wani mahauci a lokaci guda kuma dan kasuwa mai saye da sayar da dabbobi a babbar kasuwar shanu da ke Benin Jihar Edo, Alhaji Bilyamunu Gezawa ya bayyana jin dadinsa da nuna goyon bayansa shi da na kungiyarsu ta mahauta ’yan asalin jihohin Arewa da suke hade suke gudanar da sana’arsu a wuri guda a […]

‘Yanzu muka san ana dimokuradiyyar gaskiya’
‘Yanzu muka san ana dimokuradiyyar gaskiya’

Wani mahauci a lokaci guda kuma dan kasuwa mai saye da sayar da dabbobi a babbar kasuwar shanu da ke Benin Jihar Edo, Alhaji Bilyamunu Gezawa ya bayyana jin dadinsa da nuna goyon bayansa shi da na kungiyarsu ta mahauta ’yan asalin jihohin Arewa da suke hade suke gudanar da sana’arsu a wuri guda a jihar ga wannan gwamnati mai ci, inda ya kira ta da gwamnatin canji mai dinbin alheri ga talakawa da kasa baki daya.

“Wannan gwamnati ita ce muka sani gwamnatin canji ta kwarai, don haka yanzu ne muka san cewa ana mulkin dimokuradiyya na gaskiya, ba irin na kama karya ba.” Inji shi.
Ya kara da cewa, su ’ya’yan kungiyar mahuta ’yan asalin Arewa mazauna Benin, suna bai wa wannan gwamnatin goyon baya dari-bisa-dari bisa ayyukanta da ta sanya a gaba domin ci gaba al’ummar kasar nan ba tare da ta nuna wariya ba. “Muna jin dadin yadda Shugaba Muhammadu Buhari yake tafiyar da shugabancin kasar nan, canji ya zauna har abada, domin a ciki akwai zaman lafiya, wanda shi ne kashin bayan ci gaban al’umma cikin harkokinsu na rayuwa kuma akwai shirin yaki da cin hanci da karbar rashawa da suka gagari gwamnatocin da suka shude. Allah Ya taya shi rikon shugabancin Najeriya.”