Yanzu ne Buhari ke matukar bukatar addu`a

Duk wani dan kasar nan ya san cewa addu`o`i da jama`ar kasa suka dage wajen yi, da aiki tukuru, wajen tsayawa su kada kuri`unsu da tabbatar da cewa kuri`un nasu sun yi tasiri akan abin da suka zaba da kuma irin yadda Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, a karon farko ta […]

Yanzu ne Buhari ke matukar bukatar addu`a
Yanzu ne Buhari ke matukar bukatar addu`a

Duk wani dan kasar nan ya san cewa addu`o`i da jama`ar kasa suka dage wajen yi, da aiki tukuru, wajen tsayawa su kada kuri`unsu da tabbatar da cewa kuri`un nasu sun yi tasiri akan abin da suka zaba da kuma irin yadda Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, a karon farko ta bullo da tsarin yin amfani da sabon katin kada kuri`a na din-din-din da yin amfani da sabuwar na`urar tantance masu kada kuri`a a zabubbukan bana, wadannan ne suka yi sanadin da Allah SWT Ya kawo Shugaba Muhammadu Buhari da jam`iyyarsa ta adawa ta APC akan karagar mulkin kasar nan a zabubbukan bana, har ta kai ta kada jam`iyyar PDP, jam`iyyar da ke mulkin kasar nan tsawon shekaru 16, tun bayan da aka dawo da mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

Babban abin da jama`ar kasa suka yi ittifaki da shi har suka zabi Shugaba Buhari bai wuce gaskiyar shi ba fiye da sauran abokan takararsa cikin neman shugabancin kasar nan, kuma shi ne kadai zai iya ceto kasar nan daga irin mawuyacin tabarbarewar matakan tsaro da na tattalin arzikin kasa dana cin hanci da rashawa da batun rashin ayyukan yi da sauran matsaloli. Dukkan wadannan matsaloli da makamantansu da su Shugaba Buhari da jam`iyyarsu ta APC, suka yi yakin neman zabe, don haka ne ma taken jam`iyyarsu ta APC yake “canji”.
A lokacin yakin neman zabe Shugaba Buhari ya sha alwashin zai ja layi akan binciken da zai yi akan jami`an gwamnati da suka wawure kudin jama`a, inda ya rinka jaddada cewa duk binciken da suka taras ana yi akan sace kudin jama`a za a ci gaba, haka kararraki irin wadannan da suke gaban shari`a za a ci gaba da su har a yanke hukunci, wanda kuma ya yi wani ba daidai ba a zamanin gwamnatinsa zai girbi abin da ya shuka, amma zai ja layi akan binciken jami`an gwamnatocin da ya gada. Amma kuma a ganawar da ya yi da gwamnonin jihohin kasar nan 36, a ranar Talatar makon jiya, a fadarsa da ke Abuja, an ruwaito shugaban yana cewa: “Watanni uku masu zuwa zasu iya kasancewa cikin wahala, amma za a iya karbo biliyoyin Daloli, zamu kuma yi iyakacin yin mu,” inji shi.
daya daga cikin Kakakin Shugaban kasa Mista Femi Adesina, ya sanar da haka bayan wancan taro da gwamnoni a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, inda ya kara da cewa shugaban kasar ya sha alwashin ganin lalle ya kwato kudin da jami`an tsohuwar gwamnatin da ta gabata suka sace. Wadannan kalamai na Shugaba Buhari suna zuwa ne bayan da shugaban ya fara nazarin kundin karbar mulki. Shugaban Kwamitin da ya kafa don haka Alhaji Ahmed Joda ya fara bayyana masa irin mummunar barnar da gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta tafka akan cin hanci da rashawa da wawure dukiyar jama`a.
Tabbas ba sai an fadi ba, gwamnatin Buhari ta shigo a mawuyacin hali, musamman akan tabarbarewar matakan tsaro irin na `yan kungiyar Boko Haram da ta sace ko yin garkuwa da mutane da fashi da makami da ta satar danyen man fetur da ta tabarbarewar tattalin arzikin kasa, har ma an ruwaito shugaban a wajen wancan taro yana kokawa akan cewa barnar da suka taras a wannan karon har ta fi ta 1983, muni wato lokacin da suka yi wa shugaban farar hula Alhaji Shehu Shagari juyin mulki, amma kuma ya sha alwashin zasu yi iyakacin bakin kokarinsu, wajen ganin yadda za su gyara abin da za su iya gyarawa.
Babu shakka wannan bincike na kwato dukiyar talakawa da jami`an gwamnatoci suka wawushe, Na san ba zai tsaya ba akan gwamnatin Jonathan da makarrabansa ba ko gwamnonin jam`iyyarsu ta PDP ba, tabbas sai ya shafi tsofaffin gwamnonin jam`iyyar adawa ta APC da suka taru suka kafa jam`iyyar a shekarar 2013, wato ke nan har da tsofaffin gwamnonin PDP biyar da suka canja sheka zuwa APC, bayan kafuwarta.
Koda wasu gwamnonin PDP sun yaki Buhari a cikin harkokin yakin neman zabubbukan bana (abinda dama haka ya kamata a siyasance), amma ai akwai wasu gwmnonin PDP (musamman wadanda suka kammala wa`adinsu na biyu) da bayan ganin inda guguwar canjin, ke kadawa suka kuma tabbatar cewa za ta share jam`iyyarsu da dan takararsu na neman shugabancin kasa, kuma shugaban kasa a wancan lokacin wato tsohon Shugaban Jonathan, don haka suka raba kafa wajen yin angulu da kan zabo, suka taimakawa tafiyarsu da ta Buhari, har ya kai ga nasara, shi kuma Shugaba Buhari da wasu makarrabansa sun san hakan.
Kar kuma ka yi batun gwamnonin jam`iyyar APC, wadanda suka kammala wa`adinsu kuma suka yi amfani da karfinsu da jininsu da lalitar gwamnatocinsu wajen tabbatar da Buhari ya kai ga nasara. Irin wadancan gwamnonin jihohi da makarraban gwamnatinsu da yanzu ba su da rigar kariya, su shugaban ke cewa zai kwato dukiyar da suka hamdame. Tabbas yakar irin wadancan mutane babban jihadi ne da ya kamata duk wani dan kasa na gari mai kishin ci gabanta ya kamawa shugaban kasa bisa ga yadda Allah Ya bashi iko, kamar yadda Hadisin Manzo (SAW) Ya umurta akan hana barna ko wani mummunan aiki, wato kodai ya hana da hannunsa, ko da bakinsa ko kuma ya yaki abin a zuciyarsa, wanda shi ne karancin imani. Don haka a ganina yanzu Shugaba Buhari ya ke matukar bukatar addu`o`in `yan kasa ta yadda zai kai ga nasara. Allah kuma Ya ba shi nasara. Amma shi kuma akwai bukatar ya motsa ya ga cewa ya nada sakataren gwamnati da sauran mataimaka da za su rinka rage masa nauyin da ke kansa, koda bai shirya nada ministoci ba a yanzu.
Yanzu kuma bari in kawowa mai karatu martanin da na samu daga wasunku, akan makalata ta makon jiya da aka buga a wannan shafin da kuma Jaridar Leadership Hausa ta makon jiyan mai taken:-

Haba Babangida kakaki kamar ba a Kaduna kake zaune ba.
Salam Ina fatan ka sha ruwa lafiya. Na karanta martini da ka yi a jaridar Leadership Hausa, da na gama karanta sai na ji ban ji dadi ba. A ce mutum ya yi shekaru irin wannan a ce an kore shi, gaskiya ba a yi masa adalci ba. Domin Ni, na taso ina jin sunayensu. Ina masu fatan alheri, albarkacin wannan watan. Kai kuma Allah Ya saka maka da alheri.
Haruna Lipton, Badikko, Kaduna. 08062255007.

Malam Ado, ya azumi da kuma fama da jama`a? Ni ma`abucin karanta shafinka ne a jaridar Aminiya, martanin da ka yi akan Kakaki, ya yi daidai saboda Hausawa na cewa idan maye ya manta, mai da ba zai manta ba. An wayi gari saboda adawa, bayan shi Kakaki ya dawo daga Amurka har littafi ya buga. To, yanzu ya zama na gari.
Sifiyanu Aminu Gafai, Katsina, 08145681985.

Salam. Da fatan an sha ruwa lafiya. Mun ga gyara ba martani ba, Allah Ya sa wanda aka yi domin shi ya dauka. Amfanin girma ke nan, a tsawatar idan an ga ba daidai ba. Allah kara girma, fasaha, lafiya da nisan kwana amin. Nagode.
Tijjani Aminu Bichi. 09038418865.
Gaskiya ne. Na karanta tsaf. Allah Ya saka da alheri. Na gode. 070 34954433.
Allah Ya sani ma`aikatan Gida Radiyon FRCN da ke Kaduna manya da kanana wadanda suke akan aiki da wadanda suka bar aiki da yawa sun kira ni suna godiya.