Yanzu Ribadu ya zama karuwan dan siyasa ke nan?
Ma’abuta wannan fili kun san ban cika tsoma baki a harkar siyasa ba, don kada a ce Gizago na da jam’iyya ko gwani a tsakanin ’yan takara. To amma wani lokaci dole ne in yi tsokaci saboda adana tarihi da saita al’amura domin jawo hankali da tunatarwa kamar yadda na saba. Kun san dai takena […]
Ma’abuta wannan fili kun san ban cika tsoma baki a harkar siyasa ba, don kada a ce Gizago na da jam’iyya ko gwani a tsakanin ’yan takara. To amma wani lokaci dole ne in yi tsokaci saboda adana tarihi da saita al’amura domin jawo hankali da tunatarwa kamar yadda na saba. Kun san dai takena duk yadda na kai da sabo da mutum ba na raga masa, balle a ce ya kauce daga kan hanya. Ba ni da gwani duk wanda na ga alamar zai fidda jaki daga duma zan goya masa baya koda daga jam’iyya mai alamar kurege ya fito. To amma fa babu abin da na tsana a rayuwata irin dan siyasa ya zama karuwa, marar alkibla da zai rika zarya yana tsalle-tsalle daga wannan jam’iyya zuwa wancan saboda kawai yana bukatar hawa kan wani mukami.Wannan shi ne abin da fitaccen dan sandan nan da ya shugabancin Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Nuhu Ahmad Ribadu ya yi a ’yan kwanakin nan na komawa Jam’iyyar PDP, wadda ya sha bayyana ta da jam’iyyar barayi macuta.
Sakamakon yadda jama’a suka rika caccakar wannan mataki da Malam Nuhu Ribadu ya dauka ala tilas ranar Talata ya fitar da bayani don kare kansa kan wannan banbarama da ya yi ta komawa PDP.
Ga abin da yake cewa kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito: “Na san abu ne mawuyaci ku fahimci dalilin komawata wata jam’iyya. Amma ina tabbatar muku mataki ne da aka tsaya sosai aka nazarta, kuma ba na fatan in bata wa wani. Kuma ba zan yi wani abu da zai kawo gaba a tsakanina da abokaina koda daga wace jam’iyya ko addini ko yanki ko kabila suka fito.”
Sannan ya musanta wasu bayanai da aka fitar a intanet da ke cewa ya bata wasu shugabannin Jam’iyyar APC da suka hada da Gwamna Kwankwaso da takwaransa Amaechi, inda ya ce karya aka shara domin hada shi fada da abokansa. Sannan ya ce bai kamata a dauki ficewarsa daga APC a matsayin gabar siyasa a tsakaninsa da abokansa ba.
Sai ya karkare wasikar tasa da cewa: “Zan fadi mataki na gaba game da gwagwarmayar siyasata nan ba da jimawa ba. Amma a yanzu ina tabbatar muku cewa komawata (PDP) wani yunkuri ne na tabbatar da alheri, ba don son rai ba kamar yadda wasu suke fada.”
Abin da Malam Nuhu Ribadu ya manta kafin wannan bayani nasa maitarsa ta riga ta fito fili, ya riga ya yanki fom din tsayawa takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar PDP,jam’iyyar da ta sa aka kori Gwamna Murtala Nyako na APC jam’iyyar da shi Ribadu yake cikin wadanda suka yi tsaye wajen kafuwarta.
Ribadu ya manta wani na hannun damarsa, Alhaji Hamidu Mahmud ya shaida wa duniya cewa suna kamun kafa a sakatariyar PDP ta kasa, domin ta wanke shi ya tsaya takarar wanda za a gudanar nan da wata biyu, saboda dokar PDP ya nuna sai mutum ya shekara biyu a cikinta kafin ya tsaya takarar kowane mukami.
Ba komawar Nuhu Ribadu PDP ce abin damuwa ba, amma dalilin komawar ce. Don kawai ya zama Gwamna sai ya makance ya shige cikin mutanen da ya bayyana da barayi masu muguwar almundahana, kuma ba kunya ba tsoron Allah ya zo ya ce mutanen kirki ne da rana kiri-kiri.
Misali a shekarar 2011 Nuhu Ribadu ya shaida wa duniya cewa: “Jonathan yana daya daga cikin ’yan Najeriya da suka fi kowa almundahana da na taba bincika a lokacin ina EFCC, kuma matsayin almundahanarsa yana Mataimakin Gwamna abin takaici ne. PDP annoba ce, kuma wata cikakkiyar gazawa ce. Canja ta ne kawai mafita.”
To, amma yanzu saboda akwai rade-radin Shugaba Jonathan ya lamunce a ba shi kujerar Gwamnan Jihar Adamawa inda ya fito, ku saurari abin da ya fada a ranar Litinin da ta gabata: “Abu ne da babu musu, Shugaba Jonathan ya yi abin kirki ga Najeriya a cikin dan karamin lokaci, kuma ina jin shi ne amsar addu’o’in ’yan Najeriya da dama. Ba lallai ne in zama Shugaban kasa ba, amma wajibin ne in sunkuya don goyon bayan wanda ke da irin tunanina game da Najeriya. Ina tabbatar muku Shugaba Jonathan ya shallake abin da nake buri ga Najeriya.”
Babban abin burgewa tarihi yana rubuce yadda a bara Shugaba Jonathan da Ribadu suka rika caccakar juna, inda har Shugaba Jonathan ya kira Nuhu Ribadu da tantagaryar munafuki kuma karuwar siyasa. Wannan ya faru ne lokacin da Nuhu Ribadu ya caccaki Shugaba Jonathan a wata lacca da ya gabatar a Kaduna.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban kasa, Reuben Abati ya fitar a ranar 10 ga Yunin bara, Shugaba Jonathan ya ce Ribadu ba ma kawai butulu ba ne, bai ma cancanci sake rike kowane irin mukami a Najeriya ba.
Sanarwar ta ce: “Fadar Shugaban kasa ta yi fatali da karya da munafunci da da’awar neman suna da Malam Nuhu Ribadu ya yi a wata lacca da ya gabatar a Kaduna a ranar Asabar, inda ya ce Najeriya a karkashin Shugaba Jonathan kamar wani “jirgin ruwa ne da ke nutsewa,” inda azzalumar gwamnatin ta yi watsi da bukatun talakawa. Babban abin bakin ciki ne yadda Nuhu Ribadu ya koma ga kukan karya da yada karairayi da cin mutuncin zababbiyar gwamnatin kasarsa domin kawai neman tagomashi a fagen siyasa bayan ’yan Najeriya sun ki amincewa da shi a zaben 2011.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Babban abin takaici ne cewa tsohon shugaban Hukumar EFCC din da ake girmamawa yanzu ya zama karuwar siyasa ya koma yana sakin baki ba kan gado don neman goyon bayan masu zabe ga sababbin abokansa da “shugabansa” wanda ya taba bayyana shi da barawo da “bai kamata ya rike mukamin gwamnati ba. Babu shakka burin hawa mulki a makance ne ya sa Ribadu sukar gwamnatin da Shugabanta ya dawo da shi kasar nan, bayan ya tafi gudun hijira, kuma ya dawo masa da mukaminsa na aikin dan sanda don kubutar da shi daga kunyata, sannan ya mayar da korarsa daga aiki zuwa ritaya, amma yanzu ya botsare yana yin abin da zai cutar da jama’a, Don haka muna lura da wannan rashin godiya.”
Jonathan ya ce tsabagen munafunci ne ga Ribadu wanda ya gina daukacin martabarsa a matsayin mai yaki da almundahana ta hanyar kauce wa dokoki da tauye hakkin wadanda ake ganin abokan gabar gwamnatin lokacinsa ne, yanzu ya rika zargin gwamnatin da take kokarin bin doka da oda da kare hakkin jama’a da kasancewa azzaluma.
Duk da wannan asakala a tsakanin Malam Nuhu Ribadu da fadar Shugaba Jonathan sai ga shi yau Ribadu yana shaida wa duniya wai Shugaban ya samu nasara fiye da yadda shi yake fata ga Najeriya.
iya don ganin su suka haye kanta ko kuma su yi kafar ungulu idan suka kasa kaiwa ga bukatunsu.
Abin tambaya shin sunan da fadar Shugaban kasa ta sanya wa Nuhu Ribadu a bara cewa shi karuwar siyasa ne ya tabbata ke nan? Ko kuwa cewar da ta yi bai cancanci sake rike kowane irin mukami ba nan gaba zi bi ruwa tunda ya dawo PDP? Tarihi ne zai zame alkali.