Yanzu tauraron Mbappe zai haska — Ronaldo

Mbappe ya ƙulla yarjejeniyar shekara biyar da Real Madrid.

Yanzu tauraron Mbappe zai haska — Ronaldo

Tsohon ɗan wasan gaban Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya ce Kylian Mbappe ya yi farar dabara da ya koma tsohuwar ƙungiyarsa da taka leda.

Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Faransa, ya koma Real Madrid da ke Sifaniya wajen murza leda.

An kwashe shekaru kusan uku ana raɗe-raɗin zuwansa Madrid, amma sai a wannan makon ne, ya tabbatar da zuwansa ƙungiyar.

Bayan jin wannan labari ne tsohon gwarzon ɗan wasan Madrid, wanda a yanzu yake buga wa Al Nassr da ke Saudiyya ƙwallo, Cristiano Ronaldo ya aika wa Mbappe saƙon fatan alheri.

Tun asali dai, Mbappe ya ɗauki Ronaldo a matsayin abin koyinsa tun yana ƙaramin yaro mai sha’awar ƙwallo.

Sannan Mbappe bai ɓoye burinsa na son taka leda a Real Madrid ba.

Bayan raba gari da PSG, Mbappe ya koma Madrid a Litinin a hukumance, inda duka ɓangarorin biyu suka fitar da sanarwar ƙulla yarjejeniyar shekara biyar.

Mbappe ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, inda ya nuna shi yana ƙaramin yaro sanye da rigar Real Madrid, da kuma hoton gwaninsa Ronaldo a bayansa.

Ronaldo ya yi tsokaci da cewa “Yanzu zan yi [kallo]. Ina farin cikin ganin ka haskaka Bernabeu. #HalaMadrid,” kamar yadda Ronaldo ya wallafa.

Masoyan Madrid za su yi fatan ganin Mbappe ya bi sahun Ronaldo, wanda ya ci ƙwallaye 450 ya taimaka wajen cin ƙwallo 131 a wasanni 438 da ya buga wa Real Madrid.

Har wa yau, ya ci kofuna 16 a shekara tara, da kyautar gwarzon duniya sau biyar.

Sai dai a yanzu Mbappe zai fara atisaye ne da tawagar ƙasar Faransa, gabanin fara gasar cin kofin ƙasashen Turai da za a yi a Jamus.

Tuni ’yan wasan Real Madrid suka dinga aike wa Mbappe saƙon murna na zuwa ƙungiyar.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa