Yanzu ya dace Buhari ya janye tallafin mai – Bankin Duniya
Bankin Duniya ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye tallafin man fetur, “Domin kuwa dawainiyarsa ta fi alfanunsa yawa nesa ba kusa ba.”Bankin ya bayyana hakan ne a wani rahoto da ya fitar a kan tattalin arzikin Najeriya a ranar Talata, inda ya ce ana bukatar samun […]
Bankin Duniya ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye tallafin man fetur, “Domin kuwa dawainiyarsa ta fi alfanunsa yawa nesa ba kusa ba.”
Bankin ya bayyana hakan ne a wani rahoto da ya fitar a kan tattalin arzikin Najeriya a ranar Talata, inda ya ce ana bukatar samun wani sarari ta fuskar kudin shiga domin, kasar ta samu damar sararawa ta samar da muhimman abubuwan da ake bukata, kamar yadda BBC ya ruwaito.
A cewar bankin, idan Najeriya ta janye tallafin za ta samar da ayyukan yi da kuma kawar da talauci.
Rahoton ya kuma ce masu zuba jari a shirye suke su bude lalitarsu muddin suka ga alamun kudirin sabuwar gwamnatin kasar nan na samar da manufofin da suka dace da bunkatar ’yan kasuwa masu zaman kansu. Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya taba bukatar gwamnatin Buhari ta janye tallafin man, amma a lokacin gwamnatin ta nuna cewa ba ta da aniyyar janye tallafin tukuna.