YANZU-YANZU: Abba Kabir ya mayar da Muhuyi Magaji kujerarsa

Gwamnan  Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado kujerarsa ta shugabancin Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi ta cin hanci ta jihar. Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce gwamnan ya mayar da shi ne nan take bisa biyayya ga umarnin kotu. […]

YANZU-YANZU: Abba Kabir ya mayar da Muhuyi Magaji kujerarsa

Gwamnan  Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado kujerarsa ta shugabancin Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi ta cin hanci ta jihar.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce gwamnan ya mayar da shi ne nan take bisa biyayya ga umarnin kotu.

Tsohuwar gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Muhuyi Magaji daga kujerarsa.

Kotu ta ba da umarnin mayar wa Muhuyi Rimin Gado kujerarsa

Ganduje Ya Biya Muhuyi Hakkokinsa Lakadan A Kotu

Sai dai ya garzaya kotu bisa da’awar cewa an dakatar da shi ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin watan Yunin nan ne kuma kotun ta tabbatar da shi akan kujerarsa.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan