An rage kudin wutar lantarki a Najeriya

NERC ta sanar da rage kudin mita data na Band A daga Naira 225 zuwa N206.

An rage kudin wutar lantarki a Najeriya

Turken wutar lantarki

Hukumar Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta rage kudin wutar ga masu amfani da layin Band A.

NERC ta umarci kamfanonin rararba wutar lantarki da su rage kudin kowane kilowatt daga Naira 225 zuwa N206 ga kwastomomin da ke kan layin Band A.

Umarnin na daga cikin matakan da hukumar ta dauka da nufin tabbatar da samun wutar lantarki ta akalla awa 20 a kullum ga ’yan Band A.

Sanarwar da Kamfanin Rarraba Lantarki na Legas ya fitar ya ce ragin zai fara aiki ne daga ranar 6 ga Mayu, 2024, amma bai shafi kwastomomin da ke kan layin lantarki na Band B, C, D da kum E ba.

Ragin N19 da aka yi wa ’yan Band A na zuwa ne kimanin wata guda da ta yi musu karin kudin kilowatt daga N68 zuwa N225, wanda ya sha Allah-wadai daga al’umma da mahukunta.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume