An sace Sarki da matarsa a cikin fada a Nasarawa

’Yan bindiga sun sace Sarkin Gurku da ke Jihar Nasarawa tare da matarsa daga fadarsa.

An sace Sarki da matarsa a cikin fada a Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga (tsohuwar ajiya)

’Yan bindiga sun yi garkwua da Sarkin Gurku da ke Jihar Nasarawa, Alhaji Jibril Mamman Waziri, da matarsa daga fadarsa.

A cikin dare ne ’yan bindiga suka kutsa cikin fadar Sarkin Gurku da ke Karamar Hukkumar Karu ta jihar, suka yi awon gaba da shi tare da mai dakinsa, Hajiya Sa’adatu Waziri.

“Misalin karfe 10 na daren ne gungun ’yan bindigar suka zo suka yi garkuwa da Sarki da matarsa; Babu daukin da jami’an tsaro suka kawo musu, shi ya sa ’yan bindigar suka iya tafiya da su.

“Saboda haka muna rokon jami’an tsaro su gaggauta kai musu dauki su kubutar da su da wuri,” in ji wani mazaunin yankin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar hakan, inda kakakinta, DSP Rahman Nansle ya kara da cewa suna kokarin ceto basaraken da matar tasa ba tare da komai ya same su ba.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan