An yi karin kudin mitar lantarki zuwa N81,000

A lokaci guda NERC ta yi karin N23,000 a kan kudin mitar lantarki daga N58, zuwa N81,000

An yi karin kudin mitar lantarki zuwa N81,000

Turakun Lantarki

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta yi karin Naira 34,000 da kuma N21,000 a kan farashin mita.

Karin Naira 23,00o ke nan NERC ta yi a lokaci guda a farashin mitar daga Naira N58,661.69 a safiyar Laraba, ta wata sanarwa da ta fitar.

Sanarwar ta ce daga yanzu farashin mita mai amfani da layi uku ya karu zuwa N81,975.16k daga N58,661.69k.

Mita mai famni da layi uku kuma an kara kudinsa da Naira 34,000 daga N109,684.36kzuwa N143,836.10k .

Sanarwar da shugaban hukumar Sanusi Garba da Kwwamishinan Dafe Akpeneye, suka fitar sun sanar cewa karin ya dace da kamfanonin wutar lantarki da kuma masu amfani da ita.

“Zai ba wa kamfanoni damar saye da kuma gyaran mitocin da samar wa kwastomomi farashin da ya dace da su ba tare da tsawwala musu ba, a yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki a kasar,” in ji sanarwar.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo