Yadda DSS ta kama shugaban NLC Ajaero
Da sanyin safiyar Litinin jami’an DSS suka yi awon gaba da Kwamared Ajaero
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), Kwamred Joe Ajaero.
Da sanyin safiyar Litinin jami’an DSS suka yi awon gaba da Kwamred Ajaero a filin jirgin sama da ke Abuja.
DSS ta kama Ajaero ne a hanyarsa ta zuwa ƙasar Birtaniya, inda zai halarci Babban Taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya, wanda za a fara ranar Litinin ɗin a birnin London.
Majiyoyin tsaro a hedikwatar DSS da ke Abuja sun tabbatar wa Aminiya cewa Ajaero na hannunsu, sun titsiye shi da tambayoyi.
Wata majiya ta shaida mana cewa tsare Kwamred Ajaero na da nasaba da zargi da ake masa na dauƙar nauyin ta’addanci.
Ana iya tuna cewa a kwanakin baya, ’yan sanda sun tsare Kwamred Ajaero tare yi masa tambayoyi bayan sum zarge shi da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci.
A ranar 29 ga watan Agusta ’yan sanda suka yi masa tambayoyi a Abuja, daga bisani suka sallame shi.