ECOWAS ta fara sabon taro kan daukar matakin soji a Nijar
Masu juyin mulkin Nijar sun yi watsi da barazanar ECOWAS na ɗaukar matakin soji, inda suka nada ministoci
Shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Yammacin Afirka (ECOWAS) sun fara taro kan ɗaukar matakin soji da za su yi bayan cikar wa’adin kungiyar ga masu juyin mulkin kasar Nijar.
ECOWAS wadda shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta tana yin wannan zama ne bayan cikar wa’adin da ta ba wa sojojin da suka yi juyin mulkin na dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa.
- Sai da na koma cin busasshiyar shinkafa a hannun sojoji saboda azaba – Bazoum
- Gwamnatin sojin Nijar ta nada ministoci
Masu juyin mulkin Nijar sun yi watsi da barazanar ECOWAS na ɗaukar matakin soji, inda gabanin taron ƙungiyar sojojin suka kafa majalisar ministoci mai mutum 21.
Sojojin sun kuma rufe iyakokin da asararurin samaniyar ƙasar tare da barazanar yaƙar duk wanda ya nemi yin shisshigi a harkokin ‘cikin gudana kasarsu.