EFCC ta gayyaci Betta Edu kan badakalar kudin tallafi
EFCC ta gayyaci Ministar Jinkai, Betta Edu, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar kan badakar kudi Naira miliyan 585
Hukumar yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC) ta gayyaci Ministar Jinkai, Betta Edu, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar kan badakar kudi Naira miliyan 585.
Gayyatar ta zo kasa da mintuna 30 da Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Betta Edu ta hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale.
“Binciken da muke yi kan zargin ba zai yi tasiri ba idan ba a dakatar da ministar ba, domin dakatarwar za ta ba mu ’yancin yin aikinmu sosai, yadda shugaban kasa ya umarce mu,” in ji shi.
- Tinubu ya dakatar da Ministar Jinkai, Beta Edu kan badakalar N585m
- Zargin N37bn: Sadiya ta kai kanta EFCC
Jami’in ya shaida wa Aminiya cewa tun da farko hukumar ta bayar da shawarar dakatar da Betta Edu domin ba da damar gudanar da bincike kan badakalar kudin.
Majiyar ta ci gaba da cewa, hukumar ta fara aikin bincike ne nan take bayan shugaban kasar ya sa a gudanar da cikakken bincike kan zargin biyan tallafin Naira miliyan 585.189 da aka ware wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Kuros Riba, Ogun da Legas zuwa wani asusu na sirri.
Kungiyoyin farar hula, lauyoyin masu fafutuka, jam’iyyun adawa da sauransu sun yi ta kira da a sallam Beta kan badakalar.