EFCC ta gayyaci shugaban hukumar aikin Hajji kan N90bn

A safiyar Talata Jalal Arabi zai hallara a babban ofishin EFCC domin tambayoyi kan tallafin N90bn da gwamnati ta ba wa maniyyata a aikin Hajjin 2024

EFCC ta gayyaci shugaban hukumar aikin Hajji kan N90bn

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeria (NAHCON), Jalal Arabi. (Hoto: Twittter/NAHCON)

Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Kasa (EFCC) ta gayyaci Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Jalal Ahmad Arabi domin amsa tambayoyi.

EFCC ta gayyaci Jalal Arabi ne domin amsa tambayoyi kan kudaden tallafin Naira biliyan 90 da Gwamnatin Tarayya ta bayar ga maniyyata domin sauke farali.

A ranar Talatar nan zai hallara a hedikwatar hukumar da ke Abuja domin yin bayani kan yadda aka raba wa maniyyata kudin tallafin.

Wasu majiyoyi a EFCC sun shaida mana cewa binciken ya taso ne sakamakon korafe-korafen da hukumar ta samu kan shugaban na NAHCON, musamman na rashin ba wa alhazai kulawar da ta dace a aikin Hajjin na 2024.

Wata majiya a hukumar ta ce,

“Aikinmu muke yi, babu ruwan aikinmubda bambancin addini ko kabila, abin da ya dame mu shi ne dakile laifukan kudina cikin al’umma.

“Yanzu haka shugaban NAHCON zai zo ya amsa tambayoyi kan sha’anin kudade.”

Wakikinmu ya nemi karin bayani daga kakakin hukumar, Dele Oyewale, amma jami’in ya ce zai bincika.

Sai dai kuma har muka kammala wannan labarin ba mu ji daga gare shi ba.

Aminta ta ruwaito cewa Shugaban NAHCON Jalal Arabi ya sanar a Litinin cewa duk alhazan jihohi da suka sauke farali a 2024 sun samu tallafin Naira miliyan 1.6 daga Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumarsa.

Batun tallafin N90bn

Jalal Arabi ya bayyana cewa tashin Dala ya sa kudin kujerar da maniyyata suka biya, Naira miliyan 4.9 gazawa, ana bukatar kowanne ya cika miliyan N3.6.

A sakamakon hukumar ta tuntubi gwamnati domin yi wa kowane maniyyaci rangwamen farashin Dala a kan Naira 850.

Ya ce amma a maimakon haka, gwamnati ta ba wa NAHCON Naira biliyan 90 domin cika wa kowanensu saboda gibin da aka samu a sakamakon faduwar darajar Naira.

“Mun sha wahala kan yadda za a raba biliyan 90 din ta yadda zai isa a cika wa kowane maniyyaci Naira miliyan 3.6 a kan miliyan 4.9 da suka riga suka biya.

“Sai NAHCON ta shigo da duk masu ruwa tsaki ta yadda kowanne bangare zai amfana da tallafin.

“Kowane maniyyaci ya samu Naira miliyan 1.6 daga cikin tallafin biliyan 90 da gwamnati ta bayar.

“Amma wadanda suka biya ta tsarin adashin gata sun fi amfana” in ji shugaban na NAHCON.

Neman a rushe NAHCON

Ana ita tuna cewa a baya, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi kira ga da a rushe hukumar NAHCON saboda yadda ta gudanar da aikin Hajjin 2024 hajj.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin jagorantar ganin cewa an rushe hukumar.

Bago ya bayyana bacin ransa ne kan masaukin alhazai da ke tantunan alfarma a Mina, inda aka saukar da shi tare wasu gwamnoni da Shugaban Majalisar Wakilai da wasu manyan mutane daga Najeriya.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa