HOTUNA: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP

Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu a safiyar Talata.

HOTUNA: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP

An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.

Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata.

Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana  a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.

A safiyar Talata a girke jami’an tsaro a Wadata Plaza, a yayin da dandazon ‘yan tauri da bangarorin biyu ke ta kokarin shiga harabar.