Hope Uzodinma Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Imo

Uzodinma zai yi wa’adi na biyu ne a matsayin gwamnan Jihar Imo.

Hope Uzodinma Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Imo

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, ta bayyana dan takarar Jam’iyyar APC kuma gwamnan Imo mai ci Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Baturen zaɓen, Farfesa Abayomi Fashina na Jami’ar Tarayya ta Oye Ekiti ne ya bayyana Mista Uzodimma a matsayin wanda ya yi nasara, inda ya ce ɗan takarar na APC ya samu ƙuri’a 540,308.

Samanja: Tauraron wasan kwaikwayo ya rasu yana da shekaru 84

Sayen kuri’u N40,000 a zaben Bayelsa ya bar baya da kura

Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, ya zo na biyu inda ya samu ƙuri’u 71,503.

Sai kuma Achonu Nneji na Jam’iyyar LP da ya zo na uku da kuri’u 64,081.

Yanzu dai Mista Uzodinma zai yi wa’adi na biyu ne a matsayin gwamnan jihar Imo.