An janye dokar hana fita a Kaduna da Zariya
Soke dokar hana fita a garuruwan Kaduna da Zariya ta fara aiki nan take
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya cire dokar hana zirga-zirga da aka kakaba a biranen Kaduna da Zariya.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar cewa umarnin cire dokar hana fita a Kaduna da Zariya ta fara aiki nan take.
Aruwan ya bayyana cewa majalisar tsaron jihar ta kuma ba da umarnin cewa wajibi ne a samun sahalewar hukumoin da suka dace kafin gudanar da kowane irin taron jama’a a jihar.
A cewar kwamishinan,yin hakan ya zama wajibi ne domin guje wa tashin-tashina ko saba doka da oda.
- Kisan masu zanga-zanga: A hukunta jami’an tsaro —HURIWA
- ’Yan fashin daji sun ƙona gidaje 23 a Binuwai
Gwamna Uba Sani, a cewarsa, ya jinjina wa malaman addini da masru rike da sarautun gargajiya bisa muhimmiyar rawa da suka taka wajen ganin a samu dawowar zaman lafiya a yankunan da aka sanya dokar.