Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta soke lasisin Kannywood
Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin masana’antar Kannywood da gidajen Gala. Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha ne ya sanar da haka da safiyar Juma’a. El-Mustapha ya ce hakan na nufin babu wanda zai ci gaba da yin fim a jihar Kano sai ya sabunta rajista da hukumar. Abba […]
Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin masana’antar Kannywood da gidajen Gala.
Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha ne ya sanar da haka da safiyar Juma’a.
El-Mustapha ya ce hakan na nufin babu wanda zai ci gaba da yin fim a jihar Kano sai ya sabunta rajista da hukumar.
Abba El-Mustapha ya zama shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano
Wakar Cin Zarafi: ’Yan Kannywood sun caccaki Davido
Wannan soke lasisin ya shafi masu fitowa a fim, da masu shiryawa, da kasuwancinsa.
Su kuma gidajen rawar Gala an dakatar da su nan take har sai an tantance su.