Obaseki ya karbi shaidar cin zaben Edo
INEC ta ba Gwamna Obaseki da mataimakinsa Philip Shaibu takardar shaidar cin zabe
Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya karbi takardar shaidar cin zaben da ya yi a karo na biyu.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta mika masa takardar tare da mataimakinsa Philip Shaibu ranar Talata.
- Yadda Boko Haram ta kashe babban hafsan soji
- ’Yan bindiga sun mayar da mata 22,000 zawarawa a Zamfara
- Gwamna Zulum ya zabi sabon Sarkin Biu
A ranar Lahadi INEC ta sanar da cewa Obaseki ya lashe zaben gwamnan jihar karkashin inuwar jam’iyyar PDP bayan ya kayar da babban abokin takararsa, Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar PDP.
A ranar 12 ga watan Nuwamba ake sa rantsar da Obaseki domin fara wa’adin mulkinsa na biyu a Jihar ta Edo.