Jami’an tsaro sun mamaye Fadar Sarkin Kano
Jami’an tsaro sun hana Sarki Sanusi II fita daga Fadar Sarkin Kano, inda suka hana shi zuwa zuwa taron nada Hakimin Bichi
Jami’an tsaro sun yi wa Fadar Sarkin Kano ƙawanya, inda suka hana Sarki Muhammadu Sanusi II fita a safiyar Juma’ar nan.
An shiga ruɗani bayan an wayi gari da ganin motocin ’yan sun tare ƙofar Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu a safiyar nan ta Juma’a.
Aminiya ta ruwaito cewar ’yan sanda sun yi hare-haren a iska domin tarwatsa jama’a, yayin da ’yan daba yake ta kai-komo a wurin.
Hakan na faruwa ne a yayin da ake sa ran Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II zai gabatar da jawabi kan sabuwar Dokar Haraji, ke tayar da ƙura a fadin Najeriya.
Sarki Sanusi II, wanda ƙwararren masanin tattalin arziƙin da harkar banki ne, zai gabatar da jawabin ne ga wasu masana tattalin arziki a daidai lokacin da batun sabuwar dokar harajin.
Wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaron sun yi wa fadar kawanya ne domin hana sarkin zuwa garin Bichi domin naɗin shugaban ma’aikatansa Munin Sunusi, a matsayin hakimi.
Sun bayyana cewa bayan mamayar, Sarki Sunusi II ya shiga tattaunawa da hakimai da kusoshin gwamnati domin cim ma matsaya.
Wata shida ke nan da rikicin kujerar Sarkin Kano ta ki ci ta ƙi cinyewa tun bayan da gwmanatin jihar ta dawo da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16, bayan ta soke dokar masarautu shida a jihar, wadda ta nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano ma 15.
Tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, wadda ba ta ga-maciji da Gwmanati mai ci ta Abba Kabir Yusuf ce ta tsige Sanusi a matsayin Sarki na 14, ta nada Aminu Bayero a kan kujerar.