Kotu ta bayar da belin El-Rfuai
Kotu ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wanda ke fuskantar shari’a a gabata kan zargin almundahana.
A safiyar Talata kotun ta bayar da balin El-Rufai, kamar yadda wani jigo a Jam’iyyar ADC, Hayatuddeen Lawal Makarfi, ya shaida wa wakilimu bayan zaman kotun a Kaduna.
Hayatuddeen Lawal Makarfi, ya bayyana cewa kotun ta amince da bayar da balin tsohon gwamnan ne bayan sauroron bukatar hakan da lauyoyinsa suka gabatar.
Sai dai ya bayyana cewa El-Rufai zai ci gaba da kasancewa a tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gurfanar d shi, zuwa lokacin da zai cika sharuddan beli kiman 10 kotun ta sanya masa.
- Yau Kotun Ƙoli ke sauraron shari’ar Jam’iyyar ADC da DPP
- Ndume ya buƙaci Gwamnati ta ceto mutum 400 da aka sace a Ngoshe
Sai dai kuma da alamar ko da El-Rufai ya cika wadannan sharudda, hukumar ba za ta sake shi ba, kasancewar tana gurfanar da shi a wata shari’ar ta daban a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.