Mutum 2 sun mutu a rushewar bene a Kano

Benen ya rushe ne a sakamakon ruwan sama kamar da baƙin kwarya da na tsawon sa’o’i a daren

Mutum 2 sun mutu a rushewar bene a Kano

An tabbatar da mutuwar mutum biyu, wasu biyu kuma sun tsallake rijiya da baya, a sakamakon rushewar wani bene mai hawa biyu a Jihar Kano.

Da misalin ƙarfe biyu a dare kafin wayewar garin ranar Alhamis ne benen ya rushe da su a unguwar Nomansland da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.

Benen ya rushe ne a sakamakon ambaliyar ruwa, kasancewar yana kusa ne da hanyar ruwan.

Benen ya rushe ne a sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kamar da baƙin kwarya na tsawon sa’o’i a cikin daren.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da hakan a safiyar Alhamis.

Kakakin hukumar, Samun Abdullahi, ya ce an garzaya da waɗanda aka ceto daga bene d ya rushe zuwa asibiti, inda suke samun kulawa.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana