ECOWAS ta shiga taro bayan ficewar Nijar, Mali da B/Faso
Shugaban Kasar Boka Bola Tinubu yana jagorantar taron shugabannin Kungiyar Rainon Tattalin Arziƙin Yammacin Afirka a halin yanzu.
Shugabannin Kungiyar Kasashen Rainon Tattalin Arziƙin Yammacin Afirka (ECOWAS) sun shiga taro jim kaɗan bayan ficewar ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar daga cikinta.
Shugaban Najeriya Boka Bola Tinubu ne ke jagorantar da a halin yanzu take gudana a fadarsa da ke Abuja.
Taron zai mayar da hankali ne kan hadin kai da bunƙasar tattalin arzikin kasashen yankin.
Za kuma a tattauna kan tasirin ficewar ƙasashen uku daga kungiyar da kuma sake nazari kan takunkuman da kungiyar ECOWAS ta sanya musu.
Zaman zai kuma tattauna a kan matsalar ta’addanci da ke addabar yankin Sahel.
Kazalika zai mayar da hankali kan wa’adin mika mulki ga farar hula a ƙasashen kungiyar ta bai wa ƙasashen yankin da sojoji suka yi juyin mulki.
Za kuma a tattauna kan tasirin ficewar ƙasashen uku daga kungiyar da kuma sake nazari kan takunkuman da kungiyar ECOWAS ta sanya musu.