Tinubu ya aike wa majalisa karin sunayen ministoci
Tinubu ya aike da karin sunayen ne a yayin da Majalisa ke tsaka da tantance rukunin farko da ya aike mata
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika karin sunayen mutanen da yake son nadawa ministoci ga Majalisar Dattawa.
Tinubu ya aike wa majalisar sunayen ne a yayin da take tsaka da tantance karashen mutane 28 da ya aike mata da farko a ranar Laraba.
- Yanzu-yanzu: Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
- Najeriya ta yanke wutar lantarkin da take ba wa Nijar
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya mika sunayen ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio.
A makon jiya ne Tinubu ya mika wa majalisar sunayen rukunin farko na mutanen da yake son nadawa ministoci daga 25 daga cikin jihohi 36 da birnin tarayya da ke kasar — saura sunaye daga jihohi 11.
Jihohin da ake jiran ya mika sunayen ministocinsu su ne: Kano, Legas, Kebbi, Filato, Adamawa, Zamafara, Gombe, Yobe, Edo, Bayelsa, da kuma Osun.
Mutanen da ya fara bayarwa sun hada da mata bakwai da maza 21, wadanda cikinsu kuma akwai tsoffin gwamnoni hudu; ’yan majalisa masu ci uku, tsoffin ‘yan majalisa uku, hadiman shugaban kasa uku, da shugaban hukumar gwamnati daya.
A jerin sunayen da ya bayar da farko, jihohi biyu, Katsina da Kuros Riba sun samu mutum biyu kowannensu.