‘Yar aiki ta tsere da jaririn gidan da take aikatau a Kaduna

‘Yar aikin gidan ta tsere da jaririn gidan da take aiki.

‘Yar aiki ta tsere da jaririn gidan da take aikatau a Kaduna

A Unguwar Tudun Wada da ke Jihar Kaduna ce wata ‘yar aikin gida mai shekara 16 a duniya ta ta yi awon gaba da jaririn dan wata 10 a gidan da take aiki.

Bayanai sun ce uwar jaririn mai suna Fauziyya Aminu Tukur, ta bar jaririn ne a wajen ‘yar aikin yayin da tafi makaranta zana jarrabawa, amma bayan daworta sai riski gidan ba kowa.

  1. Yadda Kano ta yi cikar kwari yayin bikin ba Sarki sandar mulki
  2. Yadda El-Rufa’i ya cire dansa daga makarantar gwamnati a cikin sirri

Mahaifiyar jaririn ta bayyana wa manema labarai cewar, tana barin ‘yar aikin tare da jaririn a gidan makota, a duk lokacin da za ta je makaranta.

“Bayan na dawo daga makaranta sai na zarce zuwa gidan makociyata, sai ta shaida min bata zo ba.

“Ko da na koma gida ina tunanin ko bacci ya dauketa, na dinga bugun kofa amma shiru, sai na kira mijina yazo da makullin wajensa muna bude gida muka tarar bata ciki, mun duba ko ina bata nan,” cewarta.

Rahotanni sun bayyana cewar, ‘yar aikin gidan wadda ‘yar asalin jihar Zamfara ce, ta bar gidan da misalin karfe 8 na safiyar ranar Juma’a.

Fauziyya ta bayyana cewar ta yi bincike kafin daukar yarinyar aiki, kuma a yanzu tuni ta sanar da matar da ta kawo ta gidan aikatau.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun fara bincike domin tabbatar da sun gano duk inda ‘yar aikin ta shiga.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja