’Yar aji uku ta rasu a gobarar ɗakin kwanan ɗalibai a Jami’ar Gashua

An rufe jami’ar nan take domin kaucewa abin da zai ƙara tayar da hankali musamman a tsakanin ɗalibai.

’Yar aji uku ta rasu a gobarar ɗakin kwanan ɗalibai a Jami’ar Gashua

Wata ɗaliba ’yar aji uku ta yi gamo da ajali a dalilin wata gobara da ta ƙone ɗakunan kwanan ɗalibai a Jami’ar Tarayya da ke Gashua a Jihar Yobe.

Gobarar wadda ta auku a ranar Asabar ta ƙone ɗakunan kwana 29 da ke ɗaukar ɗalibai aƙalla 300 kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

An dai tabbatar da rasuwar dalibar mai suna Shamsiyya Murtana wadda ke karatu a sashen nazarin kimiyyar halittu da albarkatun kasa da sararin samaniya da wasu dalibai uku da suka jikkata a Babban Asibitin Gashua.

Aukuwar wannan mummunan lamari ya dimauta al’ummar jami’ar wanda ya sanya aka shiga daukar matakan gaggawa.

Tuni dai Shugaban Jami’ar, Farfesa Maimun Waziri, a madadin daukacin ma’aikata, malamai da kuma dalibai ta mika sakon jaje da alhini ga iyayen daliban da lamarin ya shafa.

Kazalika, Shugabar Jami’ar ta bayar da umarnin rufe jami’ar nan take domin kaucewa abin da zai ƙara tayar da hankali musamman a tsakanin daliban jami’ar.

Cikin wata sanarwa da magatakardan jami’ar, Dokta Abubakar ya fitar, ya ce “ana umartar ɗalibai da su tattara ina-su-ina-su su koma gida har sai an neme su.”