’Yar Arewa ta farko da ta zama Farfesar ‘Mechanical Engineering’
Ya zuwa yanzu, ita ce Injiniyar ƙere-ƙere mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta kai matsayin Farfesa. Haka zalika, ita ce mace ta uku Farfesa a Injiniyancin ƙere-ƙere a duka Najeriya.
A ranar 27 ga watan Disambar 2024, Jami’ar Bayero ta Kano ta amince da ɗaga likkafar Injiniya Umma Abdullahi zuwa matsayin Farfesa a Injiniyancin ƙere-ƙere, wato Mechanical Engineering.
Farfesa Umma Abdullahi, ta koyar da karatun Injiniya a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kafin daga bisani ta koma koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano.
Ya zuwa yanzu, ita ce Injiniyar ƙere-ƙere mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta kai matsayin Farfesa. Haka zalika, ita ce mace ta uku Farfesa a Injiniyancin ƙere-ƙere a duka Najeriya.
Wannan ne ya sa Aminiya ta tattauna da ita, domin jin tarihinta, da irin gwagwarmayar da tasha har ta kai wannan matsayi.
- An kashe mutum 18 a rikicin dodanni a Imo
- Daga ƙasashen waje Boko Haram ke samun makamai da kuɗaɗe —Shugaban sojoji
Da farko za mu so ki ba ku taƙaitaccen tarihinki?
Ni dai ’yar Kano ce. An haife ni a unguwar Sharfaɗi da ke Qaramar Hukumar Birni. Na yi makarantar firamare ta Maɗatai. Na yi Karamar Sakandare ta Sani Mai-Nagge, daga nan na wuce Sakandaren Kimiyya ta Mata da ke Kiru, inda muka zama ɗaliban farko na makarantar. Bayan na kammala, na yi karatun share fagen shiga jami’a a BUK, bayan na gama suka ba ni gurbin karatu a Injiniyancin ƙere-ƙere, wato ‘Mechanical Engineering’ a turance. A lokacin ba shi ne zaɓi na ba, na fi son kwasa-kwasai da ake gamawa da wuri, amma sai suka yi la’akari da sakamakon jarabawarmu ta share fage suka tura ni ‘Mechanical’.
Na kammala dirigi na farko a shekarar 2005. Na yi digiri na biyu a nan dai Jami’ar Bayero a Injiniyancin ƙere-ƙere ɓangaren ‘Production Option’. Daga nan na wuce ƙasar Malaysia na yi digiri na uku.
Bayan na dawo daga Malaysia, na koyar a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da ke Wudil (a yanzu Jami’ar Aliko Ɗangote) na tsawon shekara 10, daga 2007 zuwa 2017. Daga nan na koma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, na koyar na tsawon shekara shida, daga nan ne kuma na dawo Jami’ar BUK, inda na ci gaba da koyarwa.
Kafin sannan, na yi bautar ƙasa a Jihar Imo. Na kuma samu kwalin Babbar Diploma ta Koyarwa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Kano, (a yanzu Jami’ar Ilimi ta Tarayya ta Kano).
Tun bayan dawowata daga Malaysia, na mayar da hankalina sosai a kan bincike. Yawancin mutane sun taƙaita injiniyancin ƙere-ƙere iya ɓangaren Injina, amma akwai abubuwan ilimi da dama a binne a ƙarƙashinsa. Akwai irinsu ɓangaren yadda za a maida bola (juji) ta koma kuɗi, da irin yadda za a samar da madadin wutar lantarki, da dai makamantansu. A irin waɗannan bangarori na riƙa yin bincike a kai-a-kai ina kuma wallafawa, sannan ga koyar da ɗalibai da nake ci gaba da yi. Kuma bisa dokar aiki, waɗannan abubuwa su suke kai malamin jami’a ga matakin Farfesa.
Tun ina Jami’ar ABU Zariya, na kai matakin kusa da Farfesa, wato ‘associate’ a turance, a shekarar 2020. Da yake da shekarun aikina nake tafiya duk jami’ar da na koma, hakan ya sa ban fuskanci matsala ba a Jami’ar Bayero, a lokacin da na ba da takardu na domin tantancewar zama Farfesa.
An tantace takardunmu tun daga matakin tsangaya, zuwa can ƙololuwa na Jami’a. Bayan haka sai aka tura takardun wajen wasu ƙwararru a fannin da muka ƙware, waɗanda ba a jami’armu suke ba, domin su tabbatar da cancantarmu. Cikin ikon Allah, bayan an bi duk waɗannan hanyoyi aka tabbatar mun da zan iya amsa sunan Farfesa a Injiniyancin Qere-ƙere.
A yanzu dai a lissafin da aka yi, ni ce mace ta farko a Arewa da ta zama Farfesa a ɓangaren Injiniyancin Kere-ƙere, kuma ta uku a duka Najeriya.
Sannan ina da aure da ’ya’ya, har ma da jikoki.
Kin ce farko ba Injiniyancin kike so ba, to ya kika ji da aka ba ki gurbin karanta shi?
Haka ne. Amma lokacin da aka ba ni gurbin karanta shi ban ji wani abu ba. Saboda a lokacin burina kawai in yi in gama. Ni dai na san tun ina ƙarama lissafi da Physics su nafi so. Lokacin da nake firamare, malamanmu suna yabo na, har a lokacin ba na mantawa da wani malamina da yake ƙarfafa mun gwuiwa idan ya zo maka mun littafi. Haka zalika, akwai wani Malam Baba, da ya fara ba mu aiki a sakandire, da yaga hazaƙata, ya tambayi firamaren da na yi, da na gaya masa ya yi ta mamaki, don a lokacin bai ma san firamaren Maɗatai ba. A lokacin, ya ƙara mun aiki a lissafi ya ga duka na cinye. Tun daga nan ni ma na fahimci na iya lissafi. Amma da nazo Bayero, kwas da nafi so shi ne Geography, saboda ina iya gane Map a duk inda na ganshi, kuma ko na yi karatu ko ban yi ba, ina ci. Bayan shi kuma, na ji ina son Chemistry musamman a lokacin da muke karatun share fage.
Sai dai tun a lokacin ba na son Biology, saboda shi kuma zai saka ni yawan karatu. Shi kuma yawan karatu zai saka ni hadda, ni kuma ba na son duk abun da zai saka ni hadda. Saboda haka na riƙa addu’ar Allah Ya zaɓa mun abun da yafi alkhairi. Da jarabawar ta fito, na fi cin Maths da Physics, sai aka bani gurbin karatu a ‘Mechanical Engineering’. Abun da ya ƙara mun ƙarfin gwuiwa da na je ajin sai naga mu biyu kacal mata. Sai na tambayi kaina me ya sa ba a kawo mata nan? Hakan ya sa nace bari in tsaya in ga me yas a mata ba sa zuwa karatun Injiniyanci!
Ko akwai ƙalubale da kika fuskanta a lokacin da kike karatu?
E to, qalubale na farko shi ne sanyaya mun gwuiwa da mutane da dama ke yi. Ko karatu muka fito za ka ji ana cewa, ‘ke me za ki yi da ‘Mechanical Engineering’? Kenan ƙarƙashin mota za ku riƙa shiga? Aiko dai za ku sha shiga ƙarƙashin mota,’ ire-iren wannan dai. Sai nake ce musu ku bari dai mu gama tukuna, sai mu san me za a yi. Ana haka, sai zuciyata ta raya mun tunda da dai akwai ƙalubale, me zai hana na koyi abun nan da kyau in zama cikin masu koyar da ɗalibai Injiniyoyi, tun da dai ana buƙatar su a Najeriya wajen ƙere-ƙere, don ko a lokacin dai ban san wata mota ƙirar Najeriya ba.
Tun daga wannan lokaci, nake sha’awar koyarwa a wannan ɓangaren, domin guje wa ƙalubalen da jama’a suke ta hango mun wanda ni ban hango ba. Hakan ya sa na zage damtsen neman sakamako mai kyau domin samun koyarwa a jami’a. Ga kuma ƙalubalen babu mata da yawa a ajinmu, amma muna da dangantaka mai kyau da sauran ’yan aji.
Ya kika ji kasancewarki mace ta farko Farfesa a Injiniyancin Qere-ƙere daga Arewacin Nijeriya?
Na yi farin ciki sosai, saboda na san kawai wani abu ne rubutacce daga Allah, ba wai don na fi wani ba. Saboda akwai mutane da yawa da suka yi kafin ni, amma sai ka ga ba su zo nan ba, wataƙil saboda a wajen da suke aiki ba sai sun kai digiri na uku ba, ko babu buƙatar su riƙa yin bincike. Wannan mataki da na taka na ɗauke shi rubutaccen al’amari ne, Allah Ya ƙaddara na zama ta farko musamman daga Arewa.
Sannan kuma, tun a farkon karatunmu, mun zama allon kwaikwayo ga yara mata. Akwai wasu shirye-shirye da muka riƙa yi a baya, inda muka riƙa ƙarfafa gwiwar mata kan suke karantar ɓangarorin kimiyya da fasaha. Wannan ya sa nake jin Ubangiji Yana son yin amfani da ni ne wajen ƙarfafa yawan mata Injiniyoyi a nan gaba.
Wace shawara za ki bai wa ’yan uwanki mata waɗanda a da suke tsoron karatun Injiniya?
Shawarar da zan ba su ita ce su ɗauka komai zai zo musu da sauƙi. Duk yadda suke zaton karatun Injiniya ba haka yake ba. Domin sai da na shiga ciki na tabbatar da yadda abin yake. Idan an tsoratar da su game da sashin karatu a aikace (practical), to magana ta gaskiya ya ma fi daɗi sama da karatu na ciki aji (Theory).
Kawai dai ya kamata su gane ‘Mechanical’ ya rabu ɓangare daban-daban, akwai ɓangaren kayan da za a samar, akwai ɓangaren ƙerawa, akwai ɓangaren maida abu mara amfani zuwa mai amfani, da ɓangaren ƙirƙirar sabbin abubuwa.
Kamar ni, na fi maida hankali a ɓangaren kayan da ake samarwa wajen ƙere-ƙere da kuma shi kansa ƙere-ƙeren, wato Material and Manufacturing a turance. Idan za a samar da abu, za ka ba da shawarar wane kaya za a yi amfani da shi a ƙera abin da zai bada inganci. Za ka karanta siffofin kayan da za a yi amfani da shi, ka san ta yadda ya dace da abin da ake son ƙerawa. Ta wannan ilimi ne duniya ta ci gaba, saboda duk abubuwan da muke gani na fasaha a duniya, masana ilimin Material sune sirrin samar da shi.
Ko da yaushe, nakan bai wa ɗalibai misali da wayar hannu. A baya, waya ta fara da mai madannai, aka koma amfani da wadda ake taɓa gilashinta da tsinke. Daga baya basirar ƙera sabuwar waya da za a iya taɓa gilashin ta da hannu ya zo. Sai ake tunanin me za a saka a ƙarƙashin gilashin wayar da zai ke gane hannun mutum. Masu ilimi irin namu na Material su ne suka yi bincike suka gano sinadarin da ya fi dacewa wajen ingancin aikin da ake so, da sauƙin samu, da kuma rashin cutarwa. Ta haka aka samar da ‘Sensor’ da a yanzu ake sakaw a wayoyinmu na Android.
Mene ne saƙonki na ƙarshe?
To abun da zan faɗa shi ne zan yi kira ga iyaye mata, da suke ƙarfafa wa ’ya’yansu mata gwuiwa. Domin ni duk abun da na zama a rayuwa mahaifiyata ce sila. Ita ce ginshiƙi na komai. Domin kana yaro ba ka san kai waye ba, amma iyaye musamman mata saboda su suke zama da yara, suna gane ko su su waye. Idan na tashi lokacin ina makaranta, ko abu na yi na nuna ɓacin rai, mahaifiyata za ta ce, “ke da kike karatu, don Allah ki maida hankali kan karatun ki.” Mahaifayata tana son in kawar da komai da ka iya ɗauke mun hankali. Kullum abin da take so shi ne in mayar da hankalina a kan karatun da na sanya a gaba. Duk da karatunta bai yi zurfin da za ta gane ƙoƙarina ba, amma za ta ji an ce na yi ta ɗaya a jarabawa, ta ji an ce an ɗauki nauyin karatuna. To wannan abun ne ya sa ta san ashe ina gane karatu. Shi ya sa kodayaushe take ganin zan iya.
Tana ganin idan na yi karatun zan samu ci-gaba da kuma ɗaukaka, shi ya sa kullum take ƙarfafa min gwiwa. Idan na yi kamar ba zan yi ba don wani abu ya ɓata mun rai, za ta ce “Don Allah ki maida hankalinki, ni da nake miki zaton zuwa wasu matakai.” Ikon Allah, duk abin da ta furta na burinta a kaina sun tabbata. Sai dai in ce Allah Ya jiƙan iyayenmu, ya gafarta musu, domin Allah Bai nufi za ta ga wannan lokacin ba. Amma duk abin da na zama a rayuwa ita ce.
Bugu da ƙari, na samu ƙwarin gwuiwar ’yan uwa, waɗanda duk da babu iyayena, suna tare da ni, suna daɗa mara mun baya. Sai kuma uwa-uba, na samu miji mai fahimta, wanda da ma farfesa ne. Ta ɓangarensa ban samu matsala ba ko kaɗan.
A nan nake kiran mata suke duban yadda za su tsara rayuwarsu, hakan zai sa a samu yadda ake so, kamar ni dai ba ni da matsala ta kowanne ɓangare, na kula da rayuwar aurena, na kula da yarana, babu abin da ba na yi. Abin da ake so shi ne kowanne abu ka ba shi haƙƙinsa, sannan ka yi shi yadda ya dace da kuma sadaukarwa.